Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 77


Gurbin Ido 77
Viral

77

Tunda suka shiga motar ko sau daya bai sani hannunsa daga cikin nata ba,yana riqe dashi gam yana murzawa a hankali,ya dameta kan ta fada masa me yasa tadan rame ba kamar yadda ya dawo da ita ba?,ko akwai mai matsa mata?,ko makarantar babu dadi?” Tsaf ta boye idanunta cikin hijab,taqi kuma cewa komai dashi,sai ya sakar mata lallausan murmushi

“Ni bari na gaya miki….tunda ke kina boyemin,kada nace kina sona ko?” Curewa ta sakeyi waje daya dariya mai dan siririn sauti tana qwace mata,abinda ya sake jan hankalinsa a kanta kenan,ya saki murmushi shima me sautin

“Bana iya baccin,bana iya cin abinci,Allah kinji nace miki Allah,tunda kika tafi kika tafi da dukka farinciki da walwalata,har na dinga jina kamar marayan da babu uwa babu uba” kanta ta daga a hankali,bakinta ya subuce tace

“Kamar ni kenan?” Idamunta na nuna alamun rauninta,tausayinta ya tsarga masa sosai, cikin ransa yace

“Kin kusa yin dariya in sha Allah” amma a fili saiya riqe hannunta dakyau,ya jashi zuwa qirjinsa saitin zuciyarsa

“Ki daukeni kamar uwa da uba a wajenki,nayi alqawari zan cike miki dukka wani gurbi da gibi da kike dashi a rayuwarki” idanunta ta maida ta lumshe,tana jin kewarsu,maganarsa ta ta katse mata tunani

“Wannan zafin jikin tun yaushe kika fara shi?”

“Last week ne”

“Ya kamata kiga likita kenan,don kada yaci gaba” ya fada tana sanya signal a motarsa,kanta ta girgiza tana bin titin da zai kaisu gidana abbi da kallo

“Yana sauka…..amna nakeson ka daukomin,tunda na dawo ban ganta ba” fuska yadan kwabe kamar yaro qarami

“Noooo……so nake mu shiga duniyar da zata bamu nutsuwa,wadda babu kowa a cikinta daga ni sai ke” yadda yayi maganar yana rage gudun motar ya kuma sanya idanunsa cikin nata sai wani nauyin ya kamata,ta maida kanta baya ta jinginar tana rufe idanuwanta.

A parking lot na gidansa dake government road ya tsaya,sannan ya kirayi me gadin,ya gaya masa ya rufe masa gidan,idan anzo nemansa yace he’s not available😂,kasaqe mai gadin yayi yana maimaita kalmar

“Yallabai kamar wani layin waya?” Ya fada a ransa

“Jeka” ja’afar din ya fada yana sallamarsa,sai ya amsa da to yana komawa bakin aikinsa.

Yanxun ma daukar abarsa cak yayi har zuwa sassansa,tare sukayi alwala sukayi sallar la’asar data kubce musu su duka,ya waiwayo yana dubanta a hankali bayan sun isar,sai ya zame ya kashingida yana tokare jikinsa da jikinta,idanunsa a qasa

“Me zakaci?” Ta tambayeshi saboda tunawan da tayi yace bai iyacin abinci

“Anything angel,indai daga gareki ne zanci,amma for now dai barci nakeji” ya fada yana zamewa a hankali,ya aza kansa saman cinyarta kwanciyar rigingine yadda yake ganin fuskarta fes,yana kafeta da wani irin kallo,idanuwansa suna lullumshewa.

Hannunsa ya sanya ya zare tafin hannunta data rufe fuskarta dasu,muryarsa da matuqar rauni yace

“Noooo…..don Allah please ki barni na more,don Allah,badon ni ba” sai ya maida hannuwansa ya harde a qijinsa yana ci gaba da kallonta,idanuwansa na masa nauyi,wani irin barci na rinjayar idanuwan nasa,a hankali yana kallonta suna rufewa,har suka rufe gaba daya,wani daddadan baccin da ya manta rabonsa dashi yayi awon gaba dashi.

Saukar numfashin sa cikin nutsuwa ya tabbatar mata baccin yakeyi da gaske,a hankali ta sauke idanuwanta kan fuskarsa

“Ma sha Allah,fatabarakallahu ahsanul khaliqin” ya fita a bakinta,asalin kyau ta gani dab da ita cakude cikin fata chocolate color.

A hankali take qare masa kallo,kwantacciyar sumar fuskarsa mai santsi baqa sidik data sake qwawata fuskarsa,wani irin gyaran fuska yakeyi,kamar na jaruman fina finan qasar hindu,koma waye yake masa aski tabbas expert ne,ya kuma san aikinsa,bata taba damuwa da aski ko sanin me askin maza ke ciki ba,amma a yanzun askin ya burgeta sosai.

Yatsanta guda daya ta sanya tsakanin gashin girarsa masu laushi tana zagaya girar,caraf taji ya kama hannunta,ya riqe da kyau cikin tattausan tafin hannunsa,cikin murya dake cike da mayen bacci yace

“Am sorry angel,hannunkin nan mai laushi da yawa zaya hanani yin bacci,har gwara kici gaba da kallona,na baki dama,ina jinsa kamar garkuwa ne a tattare dani” yana gama fadin hakan ya sanya hannuwan nasa qasan kuncinsa yayi filo da tafin hannun nata,yana kuma sake gyara kwanciyarsa sosai cikin jikinta,kamar qaramin yaron dake jin rigima ya samu mamarsa ta dorashi kan cinyarta.

Kunya da mamakin yadda baccinsa ya katse,ya kuma fahimci kallonsa takeyi ya kamata,sai tayi shuru kawai tana murmusawa kadan kadan,har zuwa sanda itama nata baccin ya iso,ya rinjayeta,sai gashi a hankali ta kifa fuskarta a tasa,sannu a hankali suka fara musayar numfashin juna.

Shi ya fara farkawa,amma sai ya gaza motsawa saboda yadda tayi masa rumfa,cikin jikinsa ya dinga jin wani abu yana shigarsa yana ratsashi,ya dinga sauke murmushi shi kadai,zaiso su tabbata a haka,saidai kuma yana dan motsawa kadan itama ta farka,ta kuma tashi da sauri cikin kunya da mamakin yadda gaba daya tayi male male a jikinsa,daga kanta zuwa qirjinta.

Juyowa yayi sosai yana fuskantarta kamar dazun da idanuwansa da suka dan kada kadan sabida baccin daya tashi a shi

“Yunwa nakeji,please ayimin taimakon gaggawa” kai ta gyada masa tana murmushi dake nuna zallar kunya

“Uhmm madam,a taimakeni,tsohuwar yunwa ta tashi” da ido tayi masa nuni kan ya dagata,bai dagata ba ya tsareta da ido amma girki yakeso,mirginawa gefe yayi da sauri yana cewa

“Ya salam…..afwan” abinda ya bata damar tashi kenan,ta dauki ribbon dinta daya zame yayi nasa waje ta tattare sumarta mau santsi waje daya sannan ta tashi,yana kwancen har yanzu cikin mutuwar jiki yana qare mata kallo,idanuwansa suna lullumshewa,shi daya yana sake tsumuwa da ganin surarta,kasancewar yanzu babu hijabi a jikinta.

Har takai qofa taji yace cikin wata irin murya daya cika taushi da yawa

“Angel moon” sai ta tsaya cak ta waiwayo,murmushinsa shine abu na farko data fara gani sannan ya motsa bakinsa,cikin wani slow ya furta

“I love you”…..” Wani kunya ya bata yadda ya furta mata maganar,da kuma yadda ya kafeta da idanu,sai ta juya da dan sassarfa ta fita a dakin,bata tsaya ba sai datakai kitchen,sai ra jingina da freezer din cikin kitchen din tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya gami da murmushi mai taushi,ko wanne second da zaizo ya wuce mamaki J yake bata,completely ya canza,wai dama haka yake?,sai ta tuna wani hira da suka taba yi da afra,a sannan ta dauka sharrinta ne,bata gasgatata ba sai yanzu

“Hmmm,rabu da miskilallun na masu jin izza da isa,da yawansu idan kikaga yadda suku sukurkucewa akan soyayya sai sun baki tausayi,Allah saiki rainasu inda xaki gansu gaban macen da suka matowa,amma suna fitowa waje sai suyita wani izza suna muzurai” saita sauke wani sabon murmushin,ta taka zuwa tsakiyar kitchen din,kwanyarta na mata searching,cikin abubuwan data karanta a dairy din shaheeda a favourite food nashi,wanne ne mai sauqi da zata dafa masa.

Rub da ciki yayi bayan ta fita,ya jima a haka yana hasashen yadda yakeji a jikinsa akan maimunatu,da yadda soyayyarta tayi masa wani irin kamu,yana jin buqatuwa sosai zuwa gareta,saidai yanason ya bata space,kada ta dauka jikinta kawai.shine abinda yake buqata.

Toilet ya shiga yayi aswaki da miswak na Aarak,wanda indai yayi bacci irin hakan yakeyinsa,ya fesa mouth fresh a bakin nasa bayan ya daura alwala sannan ya fito,yanason ya qarar da dukka lokacinsa tare da ita.

Sam sam bataji shigowarsa ba,sai tsintar kanta tayi jingine a qirjinsa,ya zagaye ta ta qugunta,ya sanya hannuwansa saman plate tummy dinta,ya kuma dora kansa saman kafadarta yana leqen abinda take dafawa,da muryar dake wanzar da soyayya a zukata ya fara magana

“Shine kika gudu?,bayan ko kwatar abinda yake raina ban gaya miki ba?,lemme tell you one to two reasons that make me love you” sai ya sake mannata cikin jikinsa sosai kamar xai maidasu abu daya,ya sake qas da muryarsa

“I love you because you make me feel again that am worth something…..i love you because you make me smile when I almost forgotten how to…..i love you angel for so many reasons” gaba daya kalamansa sun kashe mata jiki,kawai saita kasa ci gaba da yanka dankalin da takeyi akan chopping board,tana riqe dai da wuqar kawai a hannunta.

Sakinta yayi daya lura da haka,sai ya zame ya dawo gabanta,ya karba wuqar ya fara yayyanka mata da sauri da sauri,har yadda ya iya ya bata mamaki,yana yankan yana daga kai yana kallonta kamar zata bace masa,hakan ya sanya saura kadan ya datse hannunsa,don haka ta karba aikinta tace ta gode

“Ko kin koreni ba inda zani” narai narai tayi da fuska,zuciyarta cike fal da saqonni amma kuma nauyi da kunya hadi da rashin sabon da har yanzu basuyi ba ya hanata furtawa,ya gama karantar qwayar idanunta da kyau,don haka murmushi kawai ya saki

“A juri zuwa rafi da tulu diban ruwa” ya fada a ransa.

Kusan shi ya tayata dukka aikin sukayi suka gama tare,tun cikin kitchen din ya zuba ya fara kaiwa cikinsa,itace mutum ta uku a duniya da yakejin dadin abincinsu fiye ma da yadda ransa yakeso,da qyar ya iya kaiwa falo ya zauna tayi serving nashi.

Dadin sai ya masa yawa,ya dinga jinsa yana yawo a wani gajimaren farinciki,yana ci yana kallon fuskarta har ya kammala.

Daure da babban towel ta fito a wanka bayan ta baroshi a falo yana waya,awa kusan daya kenan,a nutse ta qarasa walking closet dinsa tana dudduba kayan da zata saka,saidai babu wanda zai mata,hasalima gaba daya an kwashe sauran kayan da sukayi ragowa na mata,taja tsaki yafi a qirga,dole daga baya ta fara lalube cikin trouser dinsa ta samo daya ta saka,ya mata mugun yawa,saita tsugunna ta lanqwashe qasansa,sannan ta shiga dubawa cikin rigunansa ko zata samu wanda zata saka a jikinta.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply