Gurbin Ido Hausa Novel Hausa Novels

Gurbin Ido 80


Gurbin Ido 80
Viral

80

Tun cikin airport din malam aminu kano dake kano tana maqale dashi kamar yadda ya saba,ba ruwansa da idanuwan kowa,ta fuskanci shi din kaifi daya ne,bashi da kwane kwane ko nuqu nuqu,baya kuma iya boye abinda yake cikin zuciyarsa.

Duk yadda yayi qoqarin janta da wasa da hira don ta sake sosai amma kuma ta kasa,batasan me yasa ba gaba daya jikinta a matuqar sanyaye yake,sai faduwar gaba da takeji lokaci lokaci,a haka har jirginsu ya daga zuwa gombe.

Mota daya rak ce tazo daukansu,sanda suna cikin motar ma hannunsa na cikin nata,kanta na saman kafadarsa,idanunta na biye da titi,bata ankara cewa ba hanyar gida sukayi ba sai daga bisani,batace komai ba,duk da cikin zuciyarta zata so ace gida suka nufa ta kwanta ta huta,don wata irin gajiya takeji,kamar wadda sukayi tafiyar mota.

Tafiyar minti kusan arba’in sukayi,lokaci lokaci tana jinsa yana amsa waya,saidai batasan me yake fada ba,har suka isa wata unguwa,motar tasu ta gangara jikin wani dan symbol dake dauke da sunan street din.

Kofar wani gida suka tsaya,ta daga kanta a hankali tana duban gidan,babban gida ne da ya amsa sunansa,yana dauke da katafaren gini manyan katangu da kuma tsayayyen bene na alfarma,sauke idanunta tayi dai dai sanda security ya leqo,ba tare da yace musu komai ba kaman yasan da zuwansu ya dage musu gate suka wuce zuwa ciki kai tsaye,ya qarasa parking lot dake gefe daya na gidan can nesa kadan da gate,ya tsaida motar.

Dagata kadan ja’afar yayi yana kallonta,ya sakar mata murmushi, muryarsa a hankali yace

“What’s happening,
?” Ya tambayeta a tausashe,kawai sai ta fara tara hawaye amma kuma sai ta girgiza masa kai

“Nothing,ba komai”hannuwansa ya sanya ya kama fuskarta,ya sanya idanuwansu sosai cikin nata yana bata wani qwarin gwiwa wansa ta jishi cikin jikinta sosai,hawayen data tara suka fara shanyewa suna komawa ciki,sai da yaga ta nutsu sannan ya bita da wani murmushi mau narkar mata da zuciya

“good, everything will be fine” ya furta yana manna mata wanu kiss mai taushi a goshinta,sannan ya buda motar ya fita,ya zagaya ya bude mata,a hankali ta sauko,sai sannan ta sake kallan gidan da kyau,lallai babban gida ne

“Ki shiga ciki,yanzu zan shigo sai mu wuce gida,zaku gaisa dasu ne” kai ta gyada masa a sanyaye,tana mamakin wanne irin muhimmanci ne da mutanen har haka, wanda kai tsaye daga airport sai wajensu?,bazai bari suje gida su huta ba?.

Binta yayi da kallo sanda take takawa,cikin tafiyar nan tata kamar tana rangaji,qafafunta akan tsari,cat walking din nata tana burgeshi sosai,idanunsa basu taba ganin tafiya irin tata ba,a hankali har zuwa sanda yaga ta isa babbar qofar falon,ta bude ta shige,sai ya sauke ajiyar zuciya me nauyi yana furta

“Alhamdulillah” cikin sanyi yana kuma lumshe idanunsa,tare da jiran abinda zai biyo baya.

Cikin muryarta dake cike da sanyi tayi sallama a babban katafaren falon,dukkan mutanen dake falon suka daga kansu,banda wani babban mutum ma’abocin furfura tsalli tsalli a saman kansa dake zaune saman kujera hannunsa riqe da waya,da alama akwai wani abu me muhimmanci da yake kallo.

Da idanu ta bisu da kallo kamar wadda aka kafe daga bakin qofa,umma sa’ada ce sai anni da baaba tabawa,gefe daya dr marwan ne wato abbi a zaune,sai kuma wata dattijuwa dake zaune itama dab da babban mutumin.

A hankali ta maida dubanta ga mutum na qarshe wanda idanuwanta suka sauka a kansa,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarceta,lokaci daya taju gaba daya kwanyarta da tunaninta sun birkice,ta fidda idanunta da kyau taba qare masa kallo kamar idanuwanta zasu fado,bakinta da jikinta dukka suka fara rawa,komai dadewar zamani,komai shudewar lokaci idanuwanta da zuciyarta ba zasu taba mantawa dashi ba

“Abbuuu” ta kirayeshi da sunan da duk duniya ita daya ke kiransa dashi.

Tamkar wanda aka fusgeshi ya daga kansa da sauri,take kowanne sashe na kwanyarsa ya fara motsawa yana qoqarin dawowa saiti tare da son komawa bakin aikinta bisa tsari da doka.

Miqewa tsaye yayi bakinsa yanata motsawa,da alama akwai abinda yakeson furtawa amma kuma ya kasa cewa komai din

“Diyammm” cikin wata irin fusga ya fadi sunan,abinda ya sanya maimunatu rushewa da kuka tana sake kiran sunansa,sannan ta diba da mugun gudu tayi inda yake tsayen,saidai kafin ta qarasa ya dafe kansa da yaji kamar an balla masa qashin kansa,ya tafi luuu zai fadi,abbi da yafi kusa dashi yayi hanzarin tarbarsa,saidai tuni ya sume

“Abbuuuuu” ta sake fada da qarfi ganin ya fadi,wani irin tsoro da fargabar suna shigarta,kawai sai taji itama jiri ya kwasheta,kunnuwanta kuma suka toshe idanunta suka fara ganin gilmawar duhu,take qafafunta suka gaza daukarta,ta tafi luuu zata fadi,umma sa’ada data fisu quruciya ita ta cimmata ta tareta tana kiran sunanta da qarfin gaske,kiran da yaja hankalin ja’afar dake tsaye,ya bude idanunsa a hankali,kunnuwansa na sake isar masa da saqon kiran kunan maimunatu da akeyi,bai jira komai ba cikin wani irin hanzari da zafin nama ya nufi cikin gidan kai tsaye.

A hannun umma sa’ade ya sameta tana jijjigata gami da kiran sunanta,yana zuwa ya karbeta idanuwansa akan fuskarta da jikinta daya saki gaba daya,da alama ma batasan me ake ba

“Angel!” Shima.ya fada hankalinsa na neman gushewa daga jikinsa,ba abinda zuciyarsa ke hasaso masa sai rasata zaiyi,abbi ya kula yana neman ficewa a hayyacinsa ne,don ba abinda yake sai girgizata da kiran sunanta,da alama komai ya kwance masa

“Ja’afar!” Abbi ya kira shi da qarfi sosai,kiran daya dawo dashi hayyacinsa

“Ka dauketa ka sakata a mota,idan ka fita kace auwalu yazo yanzu yanzu mu miqasu asibiti gaba daya” cak ya dauketa kamar ‘yar tsana,yana tafiya yana kallon fuskarta,kamar idan ya daina kallonta da second daya zata mutu ne.

Cikin qasa da minti ashirin suka isa asibiti guda daya gaba dayansu,suna isa din aka karbesu aka shiga basu taimakon gaggawa gaba dayansu,abbu dai sai da aka kira likitansa da yake dubashi tsahon shekarun ya shiga dakin da aka bashi,yana da kyakkyawan hope din lafiyarsa ta dawo,tsahon shekarun dama abinda suketa lalube kenan,abinda zai tuna masa da wani.lamari daya shude a baya.

*_BAYAN AWA DAYA_*

Shuru dakin yake,babu motsin kowa duk kuwa da cewa kusan su biyar ne cikin dakin,daga saman gadon maimunatu ce kwance a miqe saman gadon,hannunta maqale da qarin ruwa,ja’afar na tsaye gaban gadon ya sanya tafin hannun da ake qara mata ruwan cikin nashi,kamar zaya koma cikinta ko kuma ya maido ciwon jikinsa,sam.ya kasa zama,baya jin nauyin kowa a lokacin,burinsa kawai shine maimunatunsa ta farka da cikakkiyar lafiya a jikinta.

Anni ammi(shiyar maman ja’afar din)baba tabawa da umma sa’ade duka suna tsaye,kowanne zuciyarsa cike da tunani iri daban daban.

Dai dai lokacin da liktar data gama dubata dazun ta turo qofar ta shigo.

Dr noor,family friend din ja’afar ce,hakanan tare sukayi primary to secondary school,yanzun haka tana da aure harda yara uku,a nutse suka gaisa dasu anni a yanzun,ba kamar dazun dako damar gaisuwar ba’a samu ba,sannan kuma kai tsaye ta wuce kan maimunatu ta dudduba file da drip din dake sauka a jikinta,tayi dan rubuce rubuce sannan ta dubi ja’afar

“Ba wani damuwa captain,komai ya dai daita,ta koma normal,tana tashi a barcin nan zakuga kamar bata yi ba,saidai idan kunga da wani matsala sai a sakemin magana,ina office dina daga nan har zuwa 10pm”

“Okay,thank you” murmushi tayi
“Babu komai captain,ba wucewa zatayi ta barka bafa” kadan ya motsa bakinsa alamun murmushi,sai ta juya wajensu anni,kafin ta sake magana hajja ta shigo,jajirtacciyar tsohuwa mai yawan tawakkali da daukan qaddara da jarrabawar rayuwa,dukka al’amuran nan sun bugeta sosai,to amma tayi qoqarin jurewa,duk da fuskarta ta nuna zallar tashin hankali,tun dazun ita da abbi da alhaj bello qani ga abbu suna can bakin qofar dakin da likitoci ke kansa,duk suka maida hankalinsu a kanta sanda tayi sallama tana nufar gadon da maimunatu ke kwance,idanuwanta a kanta,tana jin wata qaunar jikartata da ta kwashe tsahon shekaru tana addu’a a kanta,tana fatan Allah ya bayyanata,ubangiji ya zama gantanta,jikanyar tata data jima dauke da qauna da soyayyarta a cikin ruhinta,saidai batasan a inda zata cimmata ba,bare ta nuna mata gata soyayyar da kuma kulawa,har sai yau da buwayin sarki ya yanke komai.

“Hajiya,ya jikin alhajin”

“Alhamdulillahi anni,sun gama iyakacin qoqarinsu,sun kuma bada tabbacin da yardar Allah komai nasa ya koma saiti yadda yake,da zarar ya farfado zai iya tuna komai da komai”

“To alhamdulillah, Alhamdulillah” suka kusa hada bakin wajen furtawa dukka su ukun.

Dr noor ta jinjina kai itama

“Irin hakan dama yana faruwa,amma idan taimakon Allah yazo,da zarar kaga wani abu daga cikin abubuwan da suka faru a rayuwarka ta baya komai yana dawo maka,musamman wani abu da kake matuqar so ko ka damu dashi,ko kuma yake da muhimmanci”

“Haka yake,haka kam suka ce” hajja ta fada tana dora hannunta saman kan maimunatu tana shafa sumarta,fatanta itama ta tashi cikin qoshin lafiya su gana da mahaifinta.

Ja’afar bai iya matsawa a wajen ba sai data farfado,kuka ta saki sosai,duk sai suka fita suka barshi shi da ita a dakin,abinda ya bata damar kwantar da kanta a qirjinsa tana sakin kuka da gasken gaske,ganinsa ba wanda ya tuna mata dashi sai daadarta,yau ga abbun da daadarta har ta mutu tana kewarsa,yau ga abbu amma babu daada a raye a duniya

“Dama abbuu na yana nan?,dama yana raye?” Ta fada cikin sautin kuka

“Ya akayi kasan inda abbu na yake?,dama ka sanshi?” Murmushi kawai ya saki hannunsa bisa kanta yana shafawa ta sigar lallashi,bazai hanata kuka ba,saboda wani lokaci kukan rahama ne,sannan yana tuna sanda shaheeda ta rasu,daya kasa kuka qarshe shi ya zame masa ciwon damuwa,wanda da qyar da taimakon Allah da kuma shigowarta rayuwarsa al’amuransa suka dai daita

“Banason kukan nan Angel,badon kiyi kuka ba na tsaya na nemo abbunki,don kiyi farinciki ne,ki kuma rayu cikin farinciki,kukanki ko……bakisan yadda yakemin ciwo a zuciyata ba” sassauta sautin kukan tayi,duk da bata bar zubar hawayen ba.

Shi ya da kansa ya kuskure mata baki yayi mata alwala,sannan ya hada mata tea tasha sannan ya zauna gefanta yana kallonta

“Zanje gida yanzu na dawo,but da sauri sauri,me dame zan dauko miki?,baxan bari su sallameki ba saikin warke sosai” kai ta langabe a shagwabe tana jin tea din daya bata yana damunta a qirji

“Abbu na”
“Don’t worry,barci yake,ance kuma kada a tasheshi,yana farkawa zan kaiki wajensa in sha Allah” kai ta gyada masa, sukayi sallama yana kissing goshinta,sannan ya fita.
[11/25, 7:22 AM] Safiyyatulkiram:

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply