Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 20


Sakon So 20
Viral

Breakfast aka fara kawowa cikin falon dan Hajiya tace ita barata dinning ba, Maman Aneesarh tace “Aneesarh taho kisha cerelac dinki kibar Anty Lujain tayi breakfast” sauka daga jikin Lujain Aneesarh tayi ahankali mikewa tayi kaman zataje wajen Mamanta saikuma da gudu tai wajen Abee zatahau jikinshi takasa, daukanta yayi ahankali yana kallon fuskanta ahankali yace “you don’t want to eat”? Gyadamai kai tayi da sauri tana kallon Coffee dayake sha, dan murmushi yayi yakai bakinta kurba tayi kadan jin daci yasa ta tabe baki tasauka daga jikinshi tawuce wajen Mamanta.

Lujain na zaune inda take akasa atisha yazo mata hannunta takai kan fuskanta tayi tanajan hancinta saiga nabiyu yazomata shima tayi tace “Alhamdulillah” na uku na zuwa, Hajiya tace “sannu Lujain” na hudu ne yazomata shima tayi dayasa kowa ya kalleta banda Abee dake kokarin kurban coffee shi, Hajiya tace “kin kwana da AC ne Lujain”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali, hakan yasa Hajiya tace “bata farfesu da shayi tasha Binta, sannu mura keson kamata” shayi Anty Binta tahada mata mai kayan kamshi, bala’in yunwa takeji jikinta har rawa yasoma ganin shayi, Anty Binta nagamawa dasauri tadauki cup nashayin takai bakinta ta kurba wani kalan zafi dataji yasa batasan lokacin datasaki cup dinba shayin sai cinyanta wani kalan ihu ta kurma dayasa har Abee saida ya kalleta. “Wayyoooo Allah na zafi, Gwaggo” tai maganan tana kokarin kwaye doguwan rigan sama tana yarfe hannu tana kuka, Hajiya tace “daga gani bata sabashan shayi mai zafin nan ba Subhanallahi sannu ya isa daina kuka” Anty Binta ganin shirin dage rigan take yasa takai hannunta ta taba inda shayin yazuban mata tace “sannu sannu, jeki cire kayan zan biyoki da breakfsat din sama” Gyadamata kai tayi tana share hawayen daya zubomata tawuce sama da sauri tana tafiya ahankali su Sajida suka bita da harara, Anty Binta tashiga hada mata breakfsat nata a tray tace “Kausar zo dauka ki kaimata” dan turobaki tayi sannan ta tashi ahankali tazo tadauka tawuce sama daidai Abee ya mike yakalli Hajiya yace “natafi Hajiya” ahankali tace “tom Allah bada sa’a Imran” wucewa yayi yafita daga dakin suma su Hamza da Abdallah suka fice daga falon Sajida da kaman jira take su fice tace “tsakani ga Allah wlh da auren wannan yarinyar kaman buhu gwara rashin aurenta, wanan shirmen za’a bama Ya Imran a matsayin mata ai wlh ancuceshi haba mana” Zainab tace “mugun an cuceshi ma bakiga ko kallo bata isheshi ba, yarinya banda haske babu abinda ya ceceta sai shegen kiba, taga shayi jikinta har rawa yake sabida son abinci” Matar Ibro ne dake wajen tace “wlh irin kibar yarintan nan ne, nima akwai kanwata Ummie haka tun tana karama takeda irin wannan kiban kaman ana hurata tashi daya kuma ta zazzage kiban tass kaman ba itaba itama zata rame ne, kwanan nan ma tunda duk damuwa yamata yawa” cikeda kulewa Sajida tace “ba wannan ake magana ba kekuma Matar Ibro mu bama sonta amatsayin Matar Ya Imran ne, mezaiyi da yarinyar da Kausar ta girma wannan ba cuta bane” daidai nan Kausar tasauko tace “ni wlh na tsaneta Allah ya kyauta Abee dina yay rayuwa da wacce na girma amatsayin mat…..” wani mugun kallo da Hajiya tama Kausar yasa takarasa maganan tace ”zoki saka Hijabinki kibar gidan nan kitafi makaranta nasan Hamza na mota yana jiranki” ba musu ta taho hijabi ta dauka da jakanta tafice Hajiya takalli su Sajida tace “kuzo kubarmini gida babu ruwanku da yarinyar nan, babu abinda ya shafeku da ita dan haka ku kiyayeta, bansonjin wani yakara maganan ta agidan nan, ban yarda kuci zalinta ko zarafinta ba, babu ruwanku tsakaninta da mijinta Imrana shine mai ita shine mai iko da ita, koni ba zamana takeba zaman mijinta take agidan nan, koba komi I expect dukanku ku girmamata amatsayinta na Matar yayanku dan haka ku kiyaye” duk shiru sukayi Hajiya tamike tawuce dakinta.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply