Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 25


Sakon So 25
Viral

 

Inner Sanctum
Zaune yake agaban wani drawer shi kadai acikin sanctum din sanye da jersey na riga green da farin wando, an rubuta Mandawari abayan rigan, farin guy ne kal dashi siriri baida kiba ko kadan, kanshi irin wannan askin nan na yan kwallo ne anyi murde murde ajikin tarin gashin da abin yay kaman kitso dan twisting ne, wayanshi ne a hannunshi yana dubawa daidai an bude kofan sanctum din an shigo wasu players ne kusan su 13 duk sun shigo ciki suna zufa kowa yay wajen zamanshi goal keeper su yace “Man! What happen is like yau bakaine a field ba is another different person, what’s happening Bro”? Wani guy ne kamanshi daya zaune kusa dashi yana kokarin cire takalmin kwallon kafanshi mai suna Olusay yace “ai Man is going through a heart break this is the second week his stalker batamai magana tamai dropping love messages ba” wani mugun kallo Mandawari yama Olusay, yan dakin dukansu kowa barin abinda yakeyi sukayi sukataho gaban Olusay dasauri sukace “yanzu Mandawari daman yanada budurwan dayakeso”? Dan dukansu are finding it unbelievable, dan dariya yayi yace “yes” wani kalan mikewa Mandawari yayi cikin fushi yace “ubanwa yace maka sonta nake” dariya Olusay yayi sosai sannan yamike tsaye tareda cire riganshi yay hanging yajuyo yakalle team members dinsu yace “wlh mugun sonta yake na rantse amman he feel mutum irinshi mai over 400M followers can not love a girl like her shida har manyan top celebrities irinsu Kim ke sonshi amman yarasa wanda zaiso sai yarinyar nan he’s even ashame to admit sonta yake barima na nuna muku page dinta kugani kuyi following nata” yakai hannunshi zai dauki wayan Mandawari wani kalan rikemai hannu yayi yana huci yace “how many time zan gayamaka kadainamin irin abin nan Abdulaziz” cikin fushi Olusay yace “how many times zan gayamaka shi so babu two ways about it idan kanason abu kanaso ne idan bakaso bakaso ne admit cewa bawata Cinderella dream girl Allah yajarabeka da so ba, normal common girl Allah yajarabeka da so Muhammad” wani kalan mugun kallo Mandawari yamai yace “and so”? Olusay yace “dan haka kadena jan aji slide into her dm and respond to all her messages and confess your feelings Bro koba hakaba guys” duka yan team nasu sukace “hakane” daya daga cikinsu mai suna Obi yace “I can’t wait to see babe din da Man keso yanda yakema mata wulakancin nan I know she must be the most beautiful girl on earth” dan tsaki Mandawari yayi yace “you guys should stay away from me and my business” yay maganan yana cire nashi rigan ya chanza kayanshi zuwa normal Riga da wando black yadauki wani big jacket yadaura akan kayan dan sanyi akeyi a Greece thank God yau zasu koma nigeria, yana gama shiryawa aka shigo akace bus nasu is ready fita duk sukayi koda sukakai bus din shida yasaba zama da Olusay yau bai zauna wajenshi ba baya yawuce yazauna abinshi Olusay baicemai komiba.

 

Airport suka wuce business class aka biamusu dayake shida Olusay ne zasu Nigeria sauran kowa yay garinsu, saida jirgin sannan ya kwanta wayanshi yabude yashiga chat dm din Lujain yana dubawa tun 2019 tafara turamai messages har zuwa yanzu dasuke 2022 amman baitaba amsata daidai dasau dayaba, fitowa yayi yashiga Fred dinta yana duba hotunan ta, 5 pictures ne kawai tai posting, daga wanda tasaka scchool uniform sai wanda take itada Gwaggo, sai wanda tayi ranan salla da Ya Samira, saikuma wanda tayi ita kadai tayi bala’in kyau a hotunan duka pink lips dinta ya tsare da idanu kaman tasaka pink janbaki, fitowa yayi yawuce wani blog a instagram yakara bude video ta na sex video nan da yanzu zai iya cewa yakalla yakai sau 20, saikuma ahankali yafito yashiga video da blog din still sukai posting na debunking news din cewa mutumin mijinta ne ga shaida daga wajen iyayensu, jazur idanunshi sukayi har jijiyoyin kanshi suka fito kashe wayan yayi ya runtse idanu ahankali murya chan kasa yace “you are mine Lujain! You love only me! You belong to me”…
*****

Har aka tashi daga makarantan tana aji, da kyar wuraren 1 ma tafita shima cafeteria officials nasu ne sukazo suka kirata kan tazo ta amshi lunch haka taje lafiyayyen abinci aka bata da drink harda kaza ga student awajen babu ma mai kallonta haka taci tadawo aji, malaman sai nan nan da ita suke yan ajinma namata magana itane ma bata amsasu da kyau kawai duktabi ta tsargu, 4 daidai aka gama musu special lesson din aka tashi kowa yashiga daukan jakanshi banda ita dake zaune inda take saida kowa yagama fita yarage ita kadai a ajin yasa tashiga hada books nata ajaka tamaida komi saikuma tai shiru tana kallon jakan yau kwana hudu kenan bataji muryan yan gidansu ba, bata gansu ba, koda su Baba dasu Mama dasu Ya Abida basu damu da ita ba Gwaggo fa? Yanzu Gwaggo barata nemeta ba, daman da gaske takosa takadata daga gidansu shikenan batada kowa, wannan wani kalan rayuwa ne da rana daya kawai tajefa kanta? Jitake kaman tadawo da hannun agogo baya ta chanza duka abinda yafaru ranan, babu wani abu datakejin dadinshi arayuwanta, ita batada waya, ita gidan nan babu wanda zai yarda yabata wayanshi balle takira Gwaggo ma, ita school dakomima baya mata dadi yanzu sabida batada Mama ne saisa abu haka ke damunta? Inda Mamanta na raye tasan barata wahala hakaba tunda gashi yanzu ma Gwaggo batasonta kaman Mama wasu kalan hawaye masu zafine sukazo mata tundaga yatsun kafanta kawai kife kanta tayi akan kafafunta tafashe da kuka sosai Abee yadade tsaye gaban ajin yana kallon yanda takife kanta kan kafanta tana kuka sannan yadanyi gyaran murya da sauri tadago jajayen idanunta, ganin Abee yasa dasauri tashare hawayen da bayan hannu ta mike tsaye ahankali tareda daukan jakanta ahankali ta goya sannan tafara tafiya kanta akasa ta taho gaban kofan, baice mata komiba yayi gaba hakan yasa tabishi abaya har zuwa waje, mota yashiga itama tabude gaba tashiga tazauna har lokacin idanunta jazur, harzai tada mota saikuma yajuyo yakalleta bayabo ba fallasa yace “why are you crying”? Dan juyowa tayi takalleshi yanda ya tsareta da idanu saitaji takasa mai karya lips nata har rawa suke tace “kewan yan gidanmu nake……” Wani kukan ne yazo mata dasauri takife kanta kan jakan makarantan da akabata a school tafashe da kuka sosai cikin kuka tace “babu wanda ya nemeni cikinsu da Baba da Mama, dasu Ya Samira harma Gwaggo basu nemeni ba sun kawoni gidanku I am all alone babu wanda ke sona, kowa haushina yakeji, I am so scared mutane su ganni kar adinga nunani babu abinda kemini dadi, I just wish inama zan mutu maybe namaga Mamana achan naji dadi, babu wanda ke sona har Gwaggo na” tunda tafara maganan kallonta yake tabashi tausayi sosai inda Kausar dinshi ne fa in this situation, “wayace miki Gwaggon ki bata sonki” dago kanta tayi dasauri da rinannun idanunta takalleshi dauke kanshi yayi yakunna key tareda tada motan yaja motan sukabar wajen, saida suka shiga titi ahankali tace “inda tana sona dabatamin auren nan ba ni inada wanda nakeso” dan kallonta yayi saikuma yadauke kai yakalli titi kusan 3min babu wanda yace komi acikin motan kaman daga sama yace “shi kike kallo rannan abayi”? Gyadamai kai tayi dasauri tana goge hawayen kan fuskanta da bayan hannu tace “eh sunanshi Muhammad Mandawari, ni shinakeso na aura” yana kallon hanya yace “kinfadama Babanki” gyadamai kai tayi tace “eh yasani” ahankali Abee yace “to mesa basu aura miki shi ba”? Dan rage murya tayi looking so sad tace “ai baitaba amsa messages dina a instagram bane ba” batare da Abee yakalleta ba yace “do you have phone”? Girgizamai kai tayi tace “a’a da wayan Ya Samira nabude instagram nai following dinshi rannan dana fara ganinshi a tV dakin Gwaggo yana buga kwallo” “kinason kwallo”? Abee yay maganan yana kallon titi, ahankali tace “eh inason kallon kwallo kuma inason Mandawari sosai, nasan inda yau zan ganshi all my problems will be gone zaije wajen Baba yace shine zai aureni bakaiba sai ka sakeni amini aure dashi natafi wajenshi muyi zamanmu” daidainan sukakai gaban wani saloon yakashe motan yadan kalleta ganin tana kallonshi kaman tasami tV da manyan idanunta masu kala dana mage yasa yadauke kai wayanshi yadauka duk tana kallonshi komi nashi anatse yakeyi baitaba mata dogon magana ba sai yau kuma kaman magic sai yan maganganun sukasa ta manta da bakin cikin datakeyi, ijiye wayan yayi yajuyo yakalleta jin alamun ana kallonshi dasauri tadauke kai tana wasa da yatsunta, dauke kai shima yayi daidai nan Anty Binta tafito daga saloon din tazo bangaren Lujain tabude tace “Iyye yan makaranta oyoyo” murmushi Lujain tayi, Anty Binta tace “ke baki gajiya da kuka ne look at your eyes fito muje to a gyara miki gashin nan dabaki iya tajewa da kanki a kitsashi, kawo jakan nan nasa abaya Ya Imran yawuce miki dashi gida” fitowa tayi tamaida jakan baya itakuma Anty binta tazagayo ta bangaren Ya Imran tace “Yaya bamu ATM card dinka zandan yima Lujain siyayyan kaya dasauran yan kananun abubuwa na mata da batadashi” wani dan iskan kallo yamata sannan yadauki ATM card nashi yabata yace “6701 is the pin” murmushi Anty Binta tayi tace “thanks Big bro” jan motanshi yayi yawuce itakuma Anty Binta yakama hannun Lujain databi motan nashi da kallo suka wuce ciki.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply