Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 5


Sakon So 5
Viral

EPISODE 5️⃣

Exquisite world collections

Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa ko ina kike ni kuma Ina Abuja.

Wannan shine instagram handle dina.

I’m on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73

08108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.

Ahankali cikin muryan bacci wata kalan siririyan murya mai shegen dadi da zaki tace “Gwaggo yunwa” shiruu kakeji banda sound na munshari dake tashi acikin duhun dakin, cikin wani irin raw voice din nan dake nuna bacci mutum yake ko cikin bacci mutum yake maganan tace “Gwaggooooo yunwaaaaaa!” Firgigit munsharin dake tashi daga dakin dakeda duhu nan ya tsaya kaman anyi ruwa an dauke karan hannu kawai ketashi daga dakin dake nuna ana tattaba gadon alamun abu ake nema sai chan aka kunna wani bright torchlight daya wani kalan haska dakin bauuuu kaman wutan lantarki, wata tsohuwar mata ce da akalla zatai 70 kokuma 72 haka kwance kan wani makeken gado mai kyau tana sanye cikin riga bubu da zani na atampa gefenta kuma wata yarinya ce mai jiki sosai kwance ta kankame Yar tsohuwar kaman zata koma cikinta idanunta akulle tana daure da wani pink towel, kallon fuskanta yar tsohuwan tayi tace “Ohh ni Safara’u Allah ubangiji ka nunamin ranan dazanyi bacci tundaga farkon dare har karshe batare da wannan fitinanniyan yarinyar ta tadani tanajin yunwa ba, Ya ubangijin sammai da kassai Ya ubangijin dake busa numfashi rokonka nake Allah ka kawomin ranan nan da gaggawa” cikeda takaici tace “aisai kitashi ga shayinki chan cike a flask, namanki da somasa nacikin kula, buredi ma na wajen idan kuma harda shinkafa zakici to wlh dakanki zakije kitchen kidebo dan kin ganni nan ban barin gadon nan Lulu” still cikin baccin batare data bude idanunta har lokacin ba tace “Gwaggo wlh ki kawomini nan” tai maganan kaman mai shirin kuka dayasa babu shiri Yar tsohuwan takai hannayenta ta kabarda hannunta dake kan jikinta tace “aisaiki sakeni intashi yarinya kaman jikan mayu” tashi daga kan gado tayi tasauka tawuce wajen da flask da wata katuwar kula da cup da duk suke kan faranta ta duka da kyar ta dauka tazo gaban gadon ta ijiye sannan ta kalleta still idanunta arufe suke tace “tashi to kici” kaman jira take ahankali ta tashi zaune idanunta still arufe tana rike da gaban towel dinta dake shirin zamewa sannan ta gyara daurin zanin da kyau tana turo baki tashiga bude idanunta ahankali, wasu hadaddun kitson kalaba ne kan yarinyar dasuka zubo mata har tsakiyan baya an jera beads a bakin kitson kaman wata Yar yarinya, wani kalan kibane da yarinyar bana wasa ba, irin asalin yaran nan ne da ake kira da chubby, idan kaga jikinta zaka dauka she’s about to burst ne dankoni dazu dana ganta kwance kan gadon nadauka Babba ne sai yanzu dana kalli fuskanta Nagane yarinya ce da duka duka bazata wuce 19-20yrs ba, wasu kalan cat sexy eyes gareta dayasa idan ka kalli fuskanta saika kasa janye idanuwanka akanta for some seconds sabida kyawun idanunta, tanada cikan gira kuma baki sidik hakama gashin idanunta da dan siririn hancinta, tanada kumatu rubu rubu dasu that looks super cute on her dawasu kananun succulent pink lips da kana kalllonta yana bada all this kananun jariran yaran nan dakeda kiba din nan sosai, skin dinta is like butter ne ko milk banmasan yanda zan siffanta muku ba but kaganta zaka dauka idan ka latsa jikinta jini zai fito ne, everything about her is chubby harta yatsun hannuwanta dana kafafunta burbur dasu kaganta kaman zata fashe, sauka tayi ahankali daga kan gadon tana kara gyara daurin towel dinta da kyau sannan akan soft carpet din tana bude flask din ahankali duk cikin bacci itakuma Gwaggo tawuce tabude bandaki tashiga. Shayin tazuba cikin wani babban cup dayaji madara da Milo yana tururi sannan tabude babban kulan samosa ne kusan 20 aciki da naman kaza da akai pepper chicken dasu guda 5 da sauri tashigaci tass ta shanye shayin kofin takara bude flask tadeba tacika tacigaba daci itakuma Gwaggo tafito ta shimfida dadduma kawai tahau tass ta shanye shayin da samosan da duka naman gyatsa tayi sannan ta tashi tahau gado ta gyara kwanciya ta kwanta murya chan kasa cikin bacci tace “Gwaggo kizo mukoma bacci” hararanta Gwaggo tayi tace “nafila zanyi gwarama kiyi baccin ki dan kinsan da asuba zan tadaki yau monday zakuje iskuko oho dai amakaranta” dan gajeren tsaki yaja tanajan bargo ahankali akuma shagwabe tace “ni bazanje ba Mandawari na zaiyi live broadcast karfe shadaya na safe yau” hararanta Gwaggo tayi tace “asheko dake da shegen gantalallen Mandawarin daharyau baimasan ko akwai mai kamanki aduniya ba babanku zai hada yaci ubanku” murguda baki tayi tareda lumshe ido kafi kacema bacci yay awon gaba da ita ganin haka itama Gwaggo ta kishingida da bango danta dan runtsa kadan tasan inhar batahau ba nan bada jimawa ba zata tashi da kanta dan Lulu bata iya bacci bataji ta rike mutum ba tun tana yar kankanuwan ta take haka.

 

5 na asuba tabude ido ahankali takalli inda Gwaggo take kan dadduma sannan ta tashi zaune ahankali tana jaye zanin gadon tana murmushi tasauka dagakan gadon da sauri tawuce bathroom na cikin dakin da ruwan zafi tai wanka tai brush sannan tai alwala tafito daure dawani towel din bayan ta wurga wanda tacire kan washing machine tazo dakin bataga Gwaggo awajenba hakan yasa tadauki wani dogon hijabi tadaura akan towel na jikinta tahau kan dadduma, tana sallame sallan ta tashi batare datayi azkar ba tawuce tafita daga dakin tashigo falonsu wani chocolate dake kan center table na cabry diary milk tadauka da sauri tana budewa tai wajen kofa daidai nan Gwaggo tafito daga kitchen tace “ina kuma zaki gari bai gama wayewa ba Lulu”? Batare data kalli Gwaggo ba tace “wajen Ya Samira zani” baki Gwaggo tabude zatai magana amman tuni tabude kofan tafice Gwaggo tabita tana kwalamata kira tace “bazakizo kisa kaya ba da asuban nan kina yawo daga ke sai tawul babu dan kwali akanki Lujain” ko juyowa batayi takalli kakartata ba saina kara sauri datakeyi zuwa babban flat din gidan tana tafiya kaman Kazan agric dataci takoshin nan tana tafiya da kyar tana tafiya tana ballan chocolate din hannunta tanaci, gidan dan Babba ne ba laifi kana ganin yanayin tsarin gidan kasan ba laifi gidan masu rufin asiri ne daidai gwargwado, bude kofan flat din tayi tashiga dakin tsaf tsaf sai kamshi yake babu kowa afalon direct tawuce wani daki dake corridor dataji hayaniya budewa tayi tashiga da sauri tana murmushi, yammata uku ne acikin dakin dake dauke dawani babban gado na daidai rufin asiri ga daddumai da hijabai akasa kana ganinsu hancinsu zaisa kagane sudin duka sisters ne saidai su kaf dinsu black beauties ne kuma ko kadan basu da jiki kaman ita su sirara ne yammata sosai, duk kallonta sukayi suka watsar amman ko ajikinta wani kalan murmushi tayi tamaida kofan tarufe takaraso cikin dakin tana kallonsu daya bayan daya, Babban cikinsu wacce akalla zatayi shekaru 23 ne da waya ke kunnenta tace “Baby ina zuwa zan kiraka” sannan ta katse wayan takalli wacce ta shigon tace “Lujain ba jiyan nan da daddare Baba yagama miki magana kan zama da towel dakuma rashin daura dankwali ba” dan yatsine fuska tayi kaman zatai kuka ashagwabe tace “mancewa nayi ban daura dan kwallin bafa Ya Samira” dasauri wacce takira da Ya Samira tace “to towel dinfa” dan turobaki tayi tace “wlh zafi nakeji idan nasa kaya” daya daga cikin sauran biyun matan ne taja tsaki tace “yarinya gabaki daya Gwaggo tamaidata mara saiti, ba dole kidingajin zafi idan kinsa kaya ba, jibeta kaman buhu” da normally ne da yanzu tai kuka da aka kirata da buhu but yau she’s extremely happy hakan yasa tace “wlh banda lokacin ki Ya Abida amman gobe ki tareni ki kirani buhu kiga abinda zai faru” yunkurowa Abida tayi kaman zata daketa hakan yasa da sauri Lujain din takoma baya Abida tace “maimaita abinda kikace”? Dauke kai tayi dayan sister da tundazu batai magana ba tace “Ya Abida inba so kike yau duk mutafi school da bakin ciki ba kada kitaba yarinyan nan yanzu dan wlh bamuba har Baba da Mama ransu yau saiya baci akanta kindaisan fitinan Gwaggo sarai” kaman jira Lujain din take jin ankira Gwaggo kwafa tayi tace “barta ta tabani ma tagani Ya Habiba” ganin rikici zasuyi yasa Samira tace “ni dan Allah ku kyaleta zonan kifadamin meya kawoki wajena da asussuban nan keda nasan war haka baki tashi ba” murmushi tayi ta harari Abida da Habiba tawuce wajen samira kaman maison gulma tace “ni akunnenki zan gayamiki” kunnen Ya Samira tabata magana tayi mai tsawo sannan ta tashi wani mugun kallo Samira tamata tace “chabdi wlh bazan baki ba hakanan” kaman zatai kuka tace “please Ya Samira kome kikeso zan miki Allah” shiru Samira tayi tana kallonta hakan yasa tace “wlh kuwa” murmushi Samira tayi tunawa da wani abu tace “inhar kin yarda zaki fasa asusun ki kibani duka kudin ciki zan baki wlh dama banda kudin ankon Aisha kinga nasamu” kaman zatai kuka tace “kai Ya Samiraaa duka fa kikace” hararanta Samira tayi tace “ashe baki cika crush din Mandawari ba, ni wlh idan inason wani celebrity babu abinda bazan iyayi akanshi ba, kikasan ma ko a live din dazaiyi yau yaraba ticket na zuwa kallonshi a stadium idan zai buga kwallo basaikije ba, kuma yana ganinki zaice yana sonki kinga yanda kikeda kyau ne” wani kalan mugun murmushi tayi dayasa kumatunta ya lotsa abin kaman wani machine ne awajen ya bala’in haska fuskanta, Abida dakejin firansu ne ta tsoma baki tace “Ya Samira stop deceiving this girl for your personal interest, international player irin Muhammad Mandawari kyakkyawan footballer hadadde ga kudi bazai taba cewa yanason wannan buhun yarinyar ba ko itace last woman on earth wlh” wani abune yatokarema Lujain wuya tajuya tana kallon Abida dake kallonta hararanta Abida tayi tace “yarinya abincin dazataci dukanmu nan bamu iya cinshi, tsakar dare kaman diyar aljanu dansu ke fatin abinci tsakar dare haka itama ketashi taci nata, Gwaggo kawai tabude mata ciki, tayaya ma Mandawari zai dauketa? Wlh tafi karfinshi” daga Abida har Habiba suka kwashe da dariya itakuma Samira tarike nata dariyan dan tana hango samun da zatayi, Habiba dake dariya tace “Mama ma tace babu wanda zai taba cewa yana sonta balle harma Ya aureta bakiga ba duka yan class nasu nada saurayi ita mazan ajin ko kallonta ma basayi bata burgesu everybody gets irritated with cin abincin Lujain da kibanta” juyawa Lujain tayi fuuu zata fice dasauri Samira tariketa tahararesu tace “don’t mind them yan bakin cikine Mandawari will acknowledge you one day as his die hard fan sannan zai soki harma ya aureki” sosai hawaye yacika mata idanu ahankali tace “are you sure Ya Samira bazaice nacika kiba ba” murmushi Samira tamata tace “ai kiba halitta ce kuma shi so comes from heart inhar na gaskiya ne ko kinfi kowa kiba aduniyan nan he will love you and cherish you, now smile for me muje mukarasa deal din inhar zaki kawo kudin yanzu zan baki wayan ki kalli live dinshi idan nadawo daga school na karbi wayata kin yarda” dasauri ta gyadakai murmushi Samira tayi tace “to jeki kawo kudin kafin nan nagama waya da Baby” da sauri tajuya tafita su Abida suka bita da harara sukace “wawiya kawai tama dawo ta dauke ledan chocolate din nan data ijiye mana anan dan nan ba dakin kakarta bane data maida bola ba”.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply