Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 29


Saran Boye 29
Viral

No. 29

………….“Na faɗaɗa maka muhimmanci kalmar shahada ne domin kasan addinin musilinci ba abin wasa bane, sannan bautama UBANGIJI shi kaɗai bashi da abokin tarayya shine cikakken imani. Gujema shirka babba da shirka ƙarama domin dawwama da tsira wajen bautama ALLAH shi kaɗai da tabbatar da soyayyar MANZONMU a zukatanmu wajibine. Zaka karɓi kalmar shaha yanzun nan Yahya, da ga haka ka tabbatar kabar kafircema ALLAH har abada, ka tsarkake ranka da zuciyarka cewa babu wani sarki sai ALLAH, ANNABI MUHAMMADU kuma MANZON ALLAH ne”.
Kai Yoohan ya jinjina a hankali, zuciyarsa na wani irin tsitstsinkewa, tsigar jikinsa na tashi batare da yasan dalili ba. Hakama jininsa gudu yake a cikin jijiyoyinsa da sauri-sauri. Wannan yanayin sai ya saukarma jikinsa da kasala da wani rauni da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba.
Baba malam na faɗar kalmar shahada yana maimaitawa, suna kai ƙarshe sai kawai hawaye suka ɓalle masa tamkar an buɗe fanfo. Ya sakko a kujerar da yake zaune a hankali ya durƙushe ƙasa jikinsa na wani irin rawa. A matuƙar mamakin su baba malam sai gani kawai sukai ya kai goshinsa ƙasa yayi sujda.
Ɗan yatsa baba malam ya saka ya ɗauke hawayen da suka sakko masa gefen ido kaɗan. Hakama Abban Abdallah sai da hawaye suka cika masa idanu, sai jin wata irin ƙauna da soyayyar Yoohan ɗin suke tana nunkuwa a zukatansu. Kamar yanda shima ƙaunarsu ke sake masa ninƙaya a zuciya.
Koda ya ɗago da ga sujudar da yayi kamar yanda yaga baba malam yayi ɗazun sai kawai ya matsa ya rungume baba malam ɗin yana cigaba da hawaye. Sunja tsahon lokaci a haka kafin baba malam ya ɗagosa yana murmushi, yace,
“Yahya ina tayaka murna. akwai ayyuka sosai a gabanka. Amma kafin su yanzu zakayi wankan shiga musulinci”.
Cikin lunshe idanu dajin wata nutsuwa ta musamman Yoohan ya gyaɗa masa kai.

Bisa jagorancin baba malam Yoohan ya gabatar da wankan shiga musilinci, tare da tsaftace wasu najasosi dake jikinsa, kamar tarin gashin kansa, an ragesa, amma ba sosai ba, dan baba malam ya shaida masa barin gashi ado ne, sannan koyine da MANZON ALLAH (S.A.W), bama ason ayi aski tas-tas ɗin nan kai na ƙyalli. Yanke masa ƙunba. Duk da shi bama mutum bane mai tarata, tare da sauran abubuwan da suka dace su kasance a tsaftace ga ƙa’idar musilinci.
Bayan ya shirya tsaf cikin sabuwar suturarsa farar ɗanyar shadda tas, da taji ɗinkin da yay masa ɗas a jiki baba malam suka rungumesa suna sake masa marhaban da shigowa addinin gaskiya, sannan suka sake zama da shi a karo na biyu domin masa bayani akan SALLAH.
yanzu kam harda su Abba Musbahu suma sun shigo tawagar. Bayan an kawo musu breakfast sunci tare su biyar abin sha’awa. Bayyana muku irin farin cikin da nutsuwa da Yoohan ke ciki a wannan lokaci ɓata lokaci ne.
Shiru falon ya ɗauka duk suna sauraren baba malam dake zuba bayani cike da nutsuwa da ƙwarewar ilimi da sanin da ALLAH ya azurtashi da shi.
Yoohan! Sallah na nufin addu’a.
Amma a shari’ance ibada ce ma’abociyar karatu da ayyuka Keɓaɓɓu, da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato *_(ASH’HADU AN LA ILAHA ILALLAHU WA ASH’HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH)_* sai ita. kuma ita ce kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta ALLAH bai aiko mala’ika da ita ba sai ALLAH Madaukakin Sarki Ya kirawo ANNABI (SAW) a daren Isra’i da Mi’iraji ya bashi ita. Yana daga girman sallah ambatonta da ALLAH Madaukakin Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa:
{وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43]
Ma’ana: “Ku tsaida sallah”
{قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم: 31]
Ma’ana: “Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga bayina da suka yi imani su tsaida sallah”.
Da sauran wurare a cikin Alqur’ani da dama.
Annabi (SAW) yana cewa: “Bainar rajuli wabainal kufri tarkus salati” (Rawahu Muslim).
Ma’ana: “Tsakanin mutum da kafirci shine barin sallah”. Kuma ana umartar karamin yaro da yin Sallah tun yana dan shekara bakwai, kuma in ya kai shekara goma a doke shi in ya ki yi.
Sallah bata yiwuwa sai da alwala.

ALWALA:
Ubangiji Madaukakin Sarki yana cewa:
“يأيها الذين ءامنوا إذا قمتم إلى الصلوة فاغسلوا وجوهكم وأيديكم إلى المرافق وامسحوا برءوسكم وأرجلكم إلى الكعبين وإن كنتم جنبا فاطهروا وإن كنتم مرضى أو على سفر أو جاء أحد منكم من الغائط أو لامستم النساء فلم تجدوا ماء فتيمموا صعيدا طيبا فامسحوا بوجوهكم وأيديكم منه ما يريد الله ليجعل عليكم من خرج ولكن يريد ليطهركم وليتم نعمته عليكم لعلكم تشكرون” المائدة: 6.
“Ya ayyuhal lazina aamanuu izaa kumtum ilas salati fagsilu wujuuhakum wa’aydiyakum ilal maraafiki wamsahuu biru’uusakum wa’arjulakum ilal ka’abayni wa’in kuntum junuban faddahharuu wa’in kuntum marda au alaa safarin au ja’a ahadun minkum minal ga’idi au laa mastumun nisa’a falam tajidu ma’ana fatayammamu sa’idan dayyiban famsahuu biwujuuhikum wa’aydiykum minhu maa yuridul Laahu liyaj’ala alaykum min harajin walakin yuridu liyudahhirakum waliyutimma ni’imatahu alaykum la’allakum tashkuruun”. Alma’ida: 6.
“Yanzu zamuje kaga yanda ake alwala kafin salla”. Baba malam ya faɗa yana miƙewa. Gaba ɗaya suka biyosa ƙofar toilet ɗin dake cikin falon. Yayinda Yoohan da baba malam suka kasance daga ciki.
*YADDA AKE YIN ALWALA SHINE:*
1-Da farko yin niyya a zuci sannan ka ce: “Bismillahi” sannan ka wanke tafukanka na dama da na hagu kowanne sau uku(3).
2-Sannan ka debo ruwa ka kurkure bakinka ka zubar da ruwan sau uku(3).
3-Sannan ka debo ruwa ka shaka a hanci ka fatar shi ma sau uku(3).
4-Sannan ka debo ruwa ka wanke fuskarka gaba dayanta sau uku(3), a lura cewa wanke fuska yana farawa ne tun daga farkon goshinka har izuwa karkashin haba wato kusa da makoshi a tsayinta kenan, a fadi kuma tun daga gefen kunnen dama zuwa gefen kunnen hagu.
5-Sannan a wanke hannu tun daga tafuka har zuwa gwiwar hannu na dama da na hagu shima uku(3).
6-Sannan a ɗebo ruwa a yi shafar kai wato a tafin hannu a shafo tun daga farkon goshi har a kai ƙeya sannan a sake dawowa farkon goshi.
7-Sannan shafar fatar kunnuwa na dama da na hagu.
8-Sannan a wanke kafafu na dama da na hagu tun daga tafin kafa har izuwa gwiwar kafa.

*ADDU’A BAYAN KARE ALWALA:*
“أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له وأشهد أن محمدا عبده ورسوله” رواه مسلم.
“سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك” رواه الطبراني.
“Ashhadu an Laa ilaha illal Lahu wahdahu laa sharika lahu wa’ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu”. Muslim ne ya rawaito.
Ko kuma ka ce;
“Subhanakal Lahumma wabihamdika Ashhadu an Laa ilaha illa anta astagfiruka wa’atubu ilaika”. Dabarani ne ya rawaito.

“Wannan itace alwala Yahya. Da ita ake gabatar da bautar ALLAH, idan babu ita babu salla. Akwai abubuwan da suke warwareta, amma zamu ajiyesu zuwa nan gaba a neman ilimi zaka sansu. A yanzu muna tsinkayar jiran shigar lokacin azhar ne, dan a ƙa’ida ko wanne wuni musulmai na gabatar da salla sau biyar ne. Akwai nafiloli da mutum kan ƙara dasu domin samun kusanci ga UBANGIJI. Amma da waɗan nan biyar dazan lissafa maka sune wajubabbu. Wanda ya barsu ko yayi sakaci dasu, haƙiƙa bai cika cikakken musulmi ba.
*SALLOLI  WAJIBABBU:*
Ya zo a hadisin Dalhatu bin Ubaydullah cewa:
“أن أعرابيا قال: يا رسول الله ماذا فرض الله عليَّ من الصلاة؟ قال: «خمس صلوات في اليوم والليلة.. الحديث…
Ma’ana: “Cewa wani Balarabe ya ce: Ya Ma’aikin ALLAH me UBANGIJI (SWT) ya wajabta a garemu na daga sallah? Sai ANNABI (SAW) ya ce: Salloli biyar a cikin (kowane) wuni da dare”.
Salloli wajibabbu guda biyar sune: 1-Asubah, 2-Azzahar,  3-La’asar,  4-Magriba,  5-Isha’i.

*LOKATAN  SALLAH  DA ADADINSU:*

ASUBAH: Sallah ce da ake yin ta raka’a biyu, Lokacin yin ta kuma shine bayan bullowar alfijir na gaskiya. Sannan ana yin karatunta a bayyane, Fatiha da sura a kowacce raka’a sannan a yi tahiya ayi sallama.

AZZAHAR: Sallah ce da ake yin ta raka’a hudu, Lokacin yin ta yana farawa idan rana ta bar tsakiyar sama ta karkata zuwa mafadarta. Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka’o’in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka’o’in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.
Amma a ranar Juma’a sallar Azzahar tana zamowa sallar Juma’a a inda take komawa raka’a biyu kuma ana yin karatunta a bayyane, bayan liman ya kare khuduba.

LA’ASAR: Sallah ce da ake yin ta raka’a hudu, Lokacinta na farawa daga inda inuwar abu tayi daidai da tsayinsa. Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka’o’in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka’o’in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

MAGRIBA: Sallah ce da ake yin ta raka’a uku, lokacin yin ta shine idan rana ta fadi a mafadarta (a nan Najeriya fuskar yamma). Sannan ana yin karatun raka’o’i biyun farko a Fatiha da sura amma a bayyane, sai a zauna a yi tahiya sannan a mike a yi raka’a daya ta karshe a karanta Fatiha kawai a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

ISHA’I: Sallah ce da ake yin ta raka’a hudu, Lokacinta yana farawa ne idan shafaki ya buya (wato dan jaja-jajan nan na bayan faduwar rana idan gari ya fara duhu). Sannan ana yin karatunta raka’o’in biyun farko Fatiha da sura a bayyane, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka’o’in biyun karshe a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

*KIRAN SALLAH:*

الله أكبر الله أكبر
أشهد أن لاإله إلا الله
أشهد أن لاإله إلا الله
أشهد أن محمد رسول الله
أشهد أن محمد رسول الله
حى على الصلاة
حى على الصلاة
حى على الفلاح
حى على الفلاح
الله أكبر  الله أكبر
لا إله إلا الله
Allahu Akbar,
Allahu Akbar,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah,
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah,
Hayya alas-Salat,
Hayya alas-Salat,
Hayya alal-falah,
Hayya alal-falah,
Allahu Akbar
Allahu Akbar
La’ilah aillall-lah.
Wannan shi ne lafazin kiran sallah. An so ga wanda ya ji kiran ana kiran sallah ya maimaita abin da mai kiran sallar yake fada shi ma, sai a wajen fadin “HAYYA ALAL SALAT” da kuma fadin “HAYYA ALAL FALAH” a madadin ka maimaita su idan mai kiran sallah ya fade su, sai ka ce “LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH”.

*YADDA AKE YIN SALLAH:*
– Da farko sai ka fiskanci alkibla (Saitin inda Ka’aba take, anan arewacin Najeriya ana cewa Gabas domin nan ne saitin inda Ka’aba take daga nan) sai a yi ikama, ga yadda lafazinta yake:
Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah, Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah. Hayya alas-Salati. Hayya alal-falahi. Kad-kamatis-salatu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilah aillall-lahu.
Sai ka daga hannuwanka daidai kafadunka ko daidai kunnuwanka sai ka yi Kabbara wato ka ce: “Allahu Akbar”.
-Sai ka dora hannunka na dama akan hannunka na hagu a kirjinka (kabalu), ko kuma ka sake su (sadalu), duk wanda ka yi daidai ne.
-Sai ka karanta karatun bude sallah a asirce ake yinta ita ce:
“Subhankal Lahumma wabihamdika watabaraka ismuka wata’ala jadduka wala’ilaha gairuka”
ko kuma ka ce: “Allahumma ba’id baini wabaina hadayaya kama ba’adta bainal mashriki wal magribi, Allahumma nakkini min hadayaya kama yunakkal saubul abyadi minad danasi, Allahumma agsilni bil ma’i wassalji wal baradi”.
-Sannan a karanta Fatiha zuwa karshenta.
-Sannan a karanta abinda ya sauwaka na daga Alkur’ani sura ko wani sashi na sura daga Alkur’ni.
-Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” ayi ruku’u, a cikin ruku’u ana iya karanta: “Subhana Rabbiyal Azim Wabihamdihi” ko a karanta “Subbuhun Kuddusun Rabbul Mala’ikati Warruhu” gwargwadon abinda ya sauwaka.
-Sai a dago daga ruku’u ana fadar “Sami’al Lahu Liman Hamidahu” idan an dago an tsaya kafin a tafi sujjada sai a ce: “Allahumma Rabbana walakal hamdu” ko ka ce “Rabbana walakal hamdu”
-Sai kuma ayi kabbara “Allahu Akbar” a yi sujjada ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjada gwargwadon abin da ya sauwaka a (a lura cewa sujjada ana yinta akan gabobi guda bakwai, goshi tare da hanci, tafuka biyu, guiwoyi biyu da kuma kafafu biyu).
-Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada a zauna akan kafar hagu ko duwawun hagu, a dora tafuka akan cinyoyi ana fadin “Rabbigfirli” ko kuma “Allahumma Igfirli”.
-Sannan ayi kabbara “Allahu Akbar” a koma sujjada ta biyu ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjadar gwargwadon abin da ya sauwaka.
-Sannan a yi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada ta biyu, yayin mikewa zuwa raka’a ta biyu (idan an zauna dan kadan kafin mikewa raka’a ta biyu ba laifi, ana kiran wannan dan zama kadan “jalsatul istirahati”).
Sai a sake kawo raka’a kamar yadda aka yi wannan ta farko, amma idan an dago daga sujjada ta biyu a raka’a ta biyu sai a zauna kamar irin zaman da aka yi na dagowa daga sujjada ta farko a dora hannaye akan cinyoyi, sannan hannun dama ayi nuni da dan yatsa manuniya a yi karatun tahiya a wannan zama, karatun tahiya shine:
“Attahiyatu Lillah, Azzakiyatu Lillah, Addayyibatus Salawatu Lillah, Assalamu alaika ayyuhan Nabiyu Warahmatullahi Wabarakatuhu, Assalamu Alaina wa’ala ibadil Lahis Salihina, Ash’hadu an La’ilaha illal Lahu Wa’ash’hadu anna Muhammadan Abduhu warasuluhu”.
Haka ya zo a (Muwadda Malik, lafazin Umar bn Khaddab).
Idan sallar mai raka’a biyu ce, kamar sallar Asubah sai ka cikasa karatun tahiyar anan da salati Ibrahimi. Shi ne kamar haka:
“Allahumma salli ala Muhammadu wa’ala aali Muhammad kama sallayta ala Ibrahim wa’ala aali Ibrahim innaka Hamidun Majid, Wabarik ala Muhammad wa’ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim waala aali Ibrahim Innaka Hamidun Majid”.
Sai kayi sallama, ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah”. Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.
Idan kuma sallar mai raka’a uku ce kamar Magariba ko raka’a hudu kamar Azahar da La’asar da Isha’i, idan kayi kashi na farko na karatun tahiya sai ka tashi ka cikasa ragowar raka’ar da ta rage ko daya ko biyun (a lura cewa a ragowar raka’ar da ta rage bayan biyun farko Fatiha kadai za’a karanta ban da sura ko wani sashi na sura) sai ka sake zama na tahiya a karo na biyu ka cikasa tahiyar har zuwa sashi na biyu na salati Ibrahimi sannan ka yi sallama ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah” Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.

*BAYANIN SHARADAN SALLAH
Sharadan sallah sune:-*
1.Musulunci. (ba ta inganta ga wanda ba Musulmi ba).
2.Hankali (ba ta inganta ga mara hankali).
3.Tsarkin dauda: Shine tsarkake jiki da tufa da bugire na mai sallah tun daga farawa har kammalawa.
4.Tsarkin Hadasi: Shine duk abin da ke warware alwala, shima tun daga fara sallah har zuwa kammalawa. Ana bukatar wadannan tsarki a cikin kowace irin sallah ma’abociyar raku’i da kuma sujjada kai har ma wanin nan nata.
5.Shigar lokacin sallah.
6.Niyya.
7.Sitirce al’aurar namiji tana kamawa ne daga cibiya har zuwa gwiwa. Ita kuwa mace baki dayan jikinta al’aurane ga ajnabinta sai dai fuskarta da tafukan hannuwanta.
8.Fuskartar Alkibla; Sai dai in a halin rincabewar yaki ko nafila a tafiyar da ya halatta ayi kasaru kuma mutum ya zamo mahayi ne kan abin hawa.
Wanda ya yi sallah yana kallon watan alkibla ba yana mai mantawa ko rashin sani har sai da ya yi sallama, to ya saketa har abada, sai dai malamai sun yi sabani a cikin wannan hukunci, haka hukuncin ya ke idan ya zamo bai yi sani da alkiblar ba ko ya ganganta yin sallar ba a alkiblar ba.

“Yahya musulinci yana da ƙa’idoji da tsare-tsare ga komai na rayuwa musamman ma ibada. Wannan kaɗanne daga ciki nake tsakuro maka a yanzu, kafin kayi ninƙaya cikin taskar ilimi ka fahimci manufata. Inaga yanzu mataki na gaba da zamuje domin gabatowar Azhar shine karantar fatiha daga littafin ALLAH, wato Al-qur’ani. Sauran abinda zai biyo baya zamu bisa daki-daki mu tsara yanda zaka samu karantarsu. Dan zamu sake komawa baya muyi cikakken bayani akan tsarki a muhimmancin sa. Ina fatan kana fahimtar duk abinda mukeyi”.
Cikin raunin murya da sanyin gaɓoɓi Yoohan ya amsa da, “Ina fahimtar komai Uncle, ina kuma cikin ɗunbin farin ciki da kasancewata cikin wannan addini dake cike da tarin hikimomi da ƙa’idoji ababen birgewa da ƙayatarwa. Tabbas tun a yinin farko na fara cin karo da ni’imomin musulinci, ina fata da addu’ar cigaba da karo dasu har ƙarhen numfashina. A yau ina jina tamkar wani sabon hallita, tamkar ba Yoohan Goshpower ba, lallai babu abinda ya kai addinin musulinci nutsuwa da kwanciyar hankali. Ya ALLAH na gode maka da wannan ni’ima taka, ina roƙon ka cigaba da tabbatar da ita a gareni batare data yanke ba koda a sakan guda ne na rayuwata”.
Cike da farin ciki su Baba malam suka amsa masa. Handkherchief Yoohan yasa ya ɗauke hawayen da suka ciko masa idanu. Kafin ya durƙusa har ƙasa yana godiya gasu baba malam da suka zamewa rayuwarsu sandar jagora wajen jawosa daga DUHU zuwa HASKE.
Saurin ɗagosa baba malam yay ya runmesa. “Yahya bamu bane ALLAH ne, mu kawai mun kasance ne daga cikin ƙaddararka ta alkairi, ALLAH yayi maka albarka, ya share hawayenka, ya yaye maka damuwarka, ya karɓi tubanka, ya shafe zunubanka damu baki ɗaya”.
A tare suka sake amsawa da amin.

__________★★★★__________

A hotel kam hankalin su Solomon a matuƙar tashe yake da rashin ganin Yoohan. Gaba ɗaya sun tada hankalin ma’aikatan hotel ɗin da barazanarsu. Saboda maigadi ya tabbatar shi baiga fitar Yoohan ba. Hakama wanda yake a reception yace baiga fitarsa ba. Ga kuma motocinsu duk suna ajiye alamar Yoohan bai fitaba a fahimtarsu.
Ganin ƙaramar magana na neman zama babba Solomon ya kira papa ya sanar masa halin da ake ciki. Cikin matsanancin tashin hankali papa yace su kira layin Yoohan ɗin mana.
“Sir! Duk wayoyinsa na nan cikin ɗakin, shiyyasama muka fahimci bada kansa ya fitaba kenan”. Solomon da jikinsa har tsuma yake ya bama papa amsa murya na rawa. Wata wawiyar tsawa papa ya sake daka masa daga can, tare da sakin wani irin ihu tamkar zai fasa gidan.
“Solo!!!!!! Inhar yarona ya shiga wani hali na rantse muku da ALLAH duk sai na kasheku da hannuna, na baku awa biyar kacal akan nemansa. Idan har kuka bari na iso kano kuyi kuka da kanku!!….”
Ƙit ya yanke wayar batare da ya bari Solo yay ko ƙwaƙwaran numfashi ba.

Sosai hankalin Solomon ya sake ƙololuwar tashi, hakama na sauran ƴan uwansa. Dan sunsan wanene Pastor Goshpower, sun san kuma abinda zai iyayi, musamman ma akan Yoohan da duk duniya bai haɗa sonshi dana kowa ba.
Suna cikin tashin hankali da tararrabin mafita sai ga ƴan sanda kusan mota uku sun iso hotel ɗin bisa jagorancin D.p.o Emanuel.
Su masu hotel babban tashin hankalinsu kar sunansu ya ɓaci. suko su Solomon sune sukasan babban tashin hankalin da zai iya samunsu da su kansu masu hotel ɗin indai har ta tabbata anyi kidnapping ɗin Yoohan a hotel ɗin ne, kamar yanda kowa yake tunani da hasashe………….✍
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply