Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 45


Saran Boye 45
Viral

No. 45

…………Hararsa shima Richard ɗin yayi, amma sai Yoohan ya watsar da shi ya miƙe yana nufar kujerar da Aymah ke kwance a kai. Omar dake murmushi ya ƙarasa inda suke ya ajiye tiren a copy table ɗin dake gefen kujerar. Hakanne ya saka Yoohan dake tsaye yana kallon yanda take rawar sanyi zama kan hannun kujerar kaɗan shi kuma.
“Thanks you” ya faɗa a hankali yana kallon Omar. Murmushi kawai Omar yayi shi dai.
Da hannu Rich ya yafito Omar, hakanne ya sakashi nufarsa. Tambayarsa yay wacece Aymah? Dan shi harga ALLAH ya gama rikicewa. Cikin ƴar dariya Omar ya faɗa masa amaryarsu ce mana.
Sosai kuwa Rich ya waro idanu waje yana faɗin, “Are you serious?”. kai Omar ya gyaɗa masa alamar sake tabbatarwa.

Shi dai Yoohan na jinsu, amma sai bai ko waiwaye ya dubesu ba, sai ma hannu da ya kai a hankali ya janye bargon Abba da Momy ta ɗakko ta lulluɓawa Aymah. Zabura tai da sauri ta cafke hannunsa tana ƙwaɓe fuska zatai kuka. Dan a tunaninta Momy ce ma ita. Tace, “Momy Please karki cire sanyi nakeji”.
Hannunsa yay ƙoƙarin janyewa daga cikin nata amma ta riƙe gam, hakanne ya sakashi barin hannun kujerar ya dawo ta gabanta ya tsugunna. Sosai ƙamshin turarensa ya daki hancinta yanzu. Tai azamar buɗe idanunta da sukai mata nauyi, sai ko a cikin nashi.
Zabura tai da sauri tana saki masa hannu tare da wancakalar da bargon har yana rufe masa fuska. Hannunsa yasa ya janye bargon a hankali tare da saurin riƙota dan tana ƙoƙarin barin kujerar ne. Hannun taja zata fisge. Fuska a murtuke yace “ALLAH idan baki nutsu ba allura zan miki”.
Ai babu shiri tai saurin komawa ta zauna hawaye na zubo mata saman fuska da uban gudu. Ta bashi dariya amma sai baiyiba ya gimtse abarsa. Sai dai hakan bai hana lips ɗinsa motsawa ba kaɗan.
Duk da halin da take a ciki sai da ta zuba masa harara ga hawaye na zirara kuma. Dariya Richard dake kallonsu tamkar ya samu television yayi. Juyawa Yoohan yayi yay masa daƙƙuwa yana danne tasa dariyar. Sai kuma ya mike daga tsugunnon da yay a gabanta ya koma kujerar da take zaunen daf da ita, dan tazarar dake tsakaninsu kaɗance. Harara Aymah ta kuma zuba masa tana maƙurewa gefe. Shi dai bai kulataba ya ɗakko kofin shayin ya miƙa mata.
“Ban sha” ta faɗa tana kuma matse jikinta a cikin bargon. Sake tsuke fuskarsa yayi da ƙyau sannan ya kalleta, dan duk da da hausa tayi maganar sarai ya jita. Sake mika mata kofin yay tare da matso da fuskarsa gab da tata. Yace, “Silly girl! Koki karɓa ko ki sha allurai a bom-bom ɗinki yanzun nan”.
Duk da tsoratar da tayi sai da tace masa ɗan iska a zuciya, saboda kalmarsa ta ƙarshe-ƙarshe. kofin ta amsa tana hawaye da tunzura baki gaba. Shi dai bai kulata ba, sai hararar Rich da kema su Osin gulmar haɗuwar matar Yoohan ta waya da yare yayi. Richard yi yay kamar bai gansa ba ya cigaba da rattafa bayani dalla-dalla.
Nu’aymah bata son shan shayin amma tana tsoron allura, hakan yasa ta daure ta shanye duka tana hawaye. Amsar kofin yayi yana sakin wani shegen Murmushin gefen baki. Aymah kanta sai da Murmushin ya daki zuciyarta, dan tunda ta sanshi a rayuwarta bata taɓa ganin yayi murmushi ba sai yanzun. Saurin riƙe bargon da take neman rufama har kanta yayi.
“Ban gama da ke ba”. Yay maganar a hankali tamkar mai yin raɗa. Cikowa idanunta sukai da sabbin hawaye. Ta ture hannunsa dake riƙe da bargon tana faɗin, “Bana shanye ba, nifa ka takuramin da yawa, yanzu ba da bace inada aure ka daina taɓani banaso”.
Da ɗan wani salo yace, “Oh really? Smalley! Waye mijin to?”.
Sosai rawar sanyin nata ya fara raguwa, sai ma wata zufa dake taruwa mata a goshi, hakanne ya saka bakin tsiwar tata sake fitowa fiye da sanda suka shigo. Tai masa wata irin harar da ta saka tsigar jikinsa tashi tana murguɗa baki, “To ina ruwanka shugaban masu shishshigi. Idan ka gama abinda ya kawoka zaka iya tafiya”.
Bakinsa ya taɓe ya ɗauke kai tamkar bai ji mita faɗa ba. Sai ma aljihun jeans ɗin jikinsa daya laluba ya zaro ledar daya ɗakko daga mota. Wani ɗan kwalin magani ne ƙarami ya zaro. Ya fiddo maganin ciki ƴan kanana, a gaban idonta ya ɓalli ɗaya, sai taga ya rabashi biyu ya maida rabin a ramin daya ciro ya liƙe tare da sakawa a kwalin. Miƙewa yay zuwa inda Rich ke zaune har yanzu yana waya, ya halbi ƙafarsa sannan ya ɗauki gorar ruwa ɗaya cikin waɗanda aka ajiye musu ya bar wajen batare da ya kula Rich daya riƙe ƙafarsa da yaji zafin halbin da yay masa ba.
Duk abinda suke Aymah kallonsu, har addu’a tayi a ranta ALLAH yasa Richard yace sai ya rama koda sun fita ne. Cikin katse mata tunanin muguntarta ya miƙa mata maganin dake cikin hanun nasa. Baki ta buɗe zatai magana yay saurin ɗaura yatsansa kan baki yace, “Shiiii!! bana son musu malama, ki karɓa inada abinyi jirana akeyi”. Da mugunta tasa yatsu biyu zata ɗauki rabin maganin dake cikin lallausan tafin hannunsa da jini keta kai kawo tamkar zai tsillo waje. Saita haɗo da fatar hannun ta mintsina da ƙarfi. Duk da yaji zafi sai baiko motsa ba balle ya nuna yasan mi tayi. Tai masa harar gefen ido tare da jefa maganin a bakinta tana faɗin, ‘Sai shegen dauriya wai shi jarumi, ai ko baka nunaba nasan wlhy kaji zafi’ ta ƙare zancen zucin nata da jefa maganin cikin baki.
Shi dai yana kallonta ne ƙasa-ƙasa. Ya miƙa mata ruwan hannun nasa, babu musu ta amsa ta tuttula cikin baki tana yamutsa fuska tamkar zata fasa ihu. Dan shima maganin bawai tana ƙaunarsa bane ba. amma dai yafi mata sauƙi-sauƙi akan allura.
Goran ta miƙa masa, ya amsa tare da ranƙwafowa ya kama bargon ya rufa mata a jikinta yana magana kamar baya so. “Kwanta”. Bata musaba ta zame ta kwanta tare da lumshe idanunta masu cikar gashin gira dana ido.
Tasowa richard daya gama gulma a waya yayi yana gaisheta da jiki. Batare data buɗe idanunba ta amsa masa sama-sama alamar barcine mai nauyi ke fisgar idanunta.

Jin motsi a bayansu yasa duk suka juya. Momy ce ta fito akan ko zasu buƙaci wani abu. Kai Yoohan ya risinar, cike da girmamawa yace, “Aunty mu bara muje, insha ALLAH barcin da zatayi yanzu zai taimaka mata zazzaɓin kuma zai sauka, shima sanyin zata bar ji”.
Fuskar Momy da fara’a tace, “To Alhmdllh Son, mun gode sosai”.
Kansa kawai ya jinjina mata sukai mata sallama suka fice tare da Omar dake zaune a ƙofar corridor ɗin Abban yana jiransu dama. Su aunty Hibbah duk sun shige kwanciya saboda gajiya. Hakan yasa suka fice abinsu babu wata gargada

Tunda suka bar gidan bakin Richard ya kasa yin shiru wajen yaba ƙyawun Aymah, da tambayar Yoohan ya akai ya samota? Bayan yasan hausawan nan basa son bama kowa ƴaƴansu sai yarensu kawai. Tun Yoohan na sharesa harya gaji ya ɗauki Bluetooth ya maƙala a duka kunnensa alamar baya bukatar cigaba da jin surutun na Rich. Kai tsaye Hotel ɗin suka koma. Inda a canma Rich yay zaman bama su Joseph labarin matar ta Yoohan, sai dai a cewarsa ƴar karamar yarinya ce.
Ko sau ɗaya Yoohan bai saka musu baki ba, gefe ma ya koma yasa aka kawo masa coffee dan su Godwin sun cika wajen da warin giyar da suka sha harda sigari. Dan dai ita sigarin ana mata shan gayune kara ɗaya ko biyu shikenan. Giyar ce dai aka maida ruwa😖.

WASHE GARI

Washe gari da safe company ɗin da aka bama kwangilar kayan Nu’aymah suka isa gidansu Yoohan bisa address ɗin da aka basu. Wannan al’amari ya bama dangin Yoohan mamaki, dan su dai basu saba ganin hakaba. A saninsu miji shike kayan gida. Amma sai gashi su an kawo musu. Da alama kuma babban company ne.
Kiran baba malam. Yoohan yayi yana roƙonsa akan basai sun saka komai ba, shi zaiyi komai insha ALLAH. Amma sai baba malan ya nuna masa sam bazai yuwuba. Mu hausa fulani hakan al’adarmu ce, yayi haƙuri ya barmu muyi. Yanajin nauyin baba malam da kimarsa. Shiyyasa dole ya bari aka kwashe kujerun falonsa da kayan gadon dake a ɗayan ɗakin, harma dana karamin falonsa na hutawa da sai ya bushi iska yake shigarsa duk suka fidda. A wani sashe na cikin gidan aka maida kayan, su kuma suka shiga aikinsu cike da ƙwarewa. Kayane ƴan ubansu masu shegen tsada. Dan sai dama suka bama Yoohan ɗin zaɓin waɗanda yake so ta hanyar pictures sannan suka koma company suka ɗakko akazo aka shiga hadawa.
Zuwa lokacin kuma gidan nasu ya fara ɗaukar baƙi na nesa. Dan sosai Papa da su Gebrail sukai gayya, hakama su Richard sun bala’i-bala’in gayyato abokansu kamar hauka. Harda na ƙasashen ƙetare. Shi angonma baisani ba, iya waɗanda kawai ya gayyata ne yasan da zuwansu.

Anan gidansu Abdallah ma ragal Aymah ta tashi, sai dai rashin ƙwarin jiki da ƴar fargabar tunanin wanda ya kasance mijin nata. duk da ranta yafi bata Yah Ab, ganin an kawota gidansu ne na nan abuja.
Gari na fara haske Aunty hibbah ta fara mata gyaran jiki na musamman, hakan yasa bataga idanun su Adawiya ba. Koma nace Adawiya kawai dan su Yusrah da Amal suna nane da ita.
Ji tai duk kewar su Umm ta gallabeta, ta amshi wayar Yusrah tai kiran baba malam, ALLAH yasa lokacin yana gida bai fita ba. Shima yaji daɗin jin muryarta, dan Abba ya sanar masa jiya tayi zazzaɓi sai da Yoohan yazo ya dubata. Sai dai kuka data saka masa ne ya sashi fara mata faɗa, daga ƙarshe kuma yay mata nasiha mai haɗe da lallashi. Yace bazai bama Umm wayarba sai idan ya kirata anjima yaji bata kukan. daga haka ya yanke kiran itama ta ajiye tana sharar ƙwallan da har yanzu sun ƙi tsayawa. Sosai Yusrah da Amal ke tausayinta. Shiyyasa duk sai suka zama shiru-shiru suma.

________★★★★________

Kasancewar su dai basusan da zaman dinner ɗin da gidansu Yoohan ke shiryawaba ƙarfe huɗu suka shirin miƙa amarya ɗakinta. Dan jirgin 8pm zasubi ya maidasu kano. Anayin sallar la’asar kuwa aunty Aysha ta tsaya akan Aymah sai da taga ta shirya tsaf cikin lifaya fara da kwalliyar golden. Tai mata ƴar kwalliya duk da ta nuna bataso. Kowa ya ganta sai ya ambaci masha ALLAH, ga uban ƙamshi da take zubawa kamar gidan turaren (miss xoxo😚lol).
Kamar yanda tsarin yake ga duk amaryar da za’a miƙa gidan miji a gidansu haka itama akai mata. Dan kuwa Abba ne yay mata rakkiya gidan aurenta sai su Momy dasu Aunty Hibbah. Su Adawiya ma Abba cayay bazasu je ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu dan bandasu za’a koma kano dama. Zasu ɗanyi kwana biyu a nan.

An tarbesu yanda basuyi zato da tsammani ba, ba kuma komai ya jawo hakanba sai dogon gargaɗin da papa da Yoohan ɗin sukayi, sai kuma sauran matan su Uncle Mike suma sunsha gargaɗi wajen mazajen nasu. Shiyyasa suka zama gaba-gaba wajen ƴan amsar amarya basu bari su mama debora sun kwafsa ba. Koba komai dangin Nu’aymah sunji ƴar nutsuwa, sai dai har cikin ransu sunji tausayinta na zama cikin waɗan nan gurguzin kahiran da idanunsu ke buɗe da wayewar karatu dana kuɗi. Amma sun rigada sunyi imani da cewar UBANGIJIN daya ƙaddara shigowarta cikinsu, yafisu sanin alkairi da hikimar yin hakan. Sun sake mata nasiha sosai, tanata kuka dai duk da bata fahimci ina aka kawota ba.
Duk da tarin abinci da kayan sha da aka kawo musu basu taɓa komaiba, sai ma miƙewa da sukayi da zummar tafiya bayan sun leƙa ko ina na sashen nata sukaga yanda company ya tsarashi gwanin birgewa. Ƴan gyare-gyaren da suka ƙara mata ba wasu masu yawa baneba, shiyyasa basu jasu lokaci ba.
Ganin suna shirin tafiya kamar yanda Abba daya fita tuni suna tare da papa a harabar gidan papa yace ya zasu tafi bayan ana shirin yin taro suma anan.
Murmushi Abba yayi, yace, “Ai su anjima kaɗanma zasu koma kano, muna musu fatan alkairi dai”. Yoohan da duk ke saurarensu yay saurin cewa, “Uncle Please ka barsu, na maka alƙawarin insha ALLAH zasu sami jirgin safe saisu wuce. Itama zata damu idan taga babu family nata a wajen”.
Ɗan jimmm Abbah yayi yana nazari, yasan gaskiya Yoohan ɗin ya faɗa, duk da dai su ba ɗabi’arsu bace yin wannan bidi’oin, to amma a yanzu basu da iko akan Aymah tunda sun kawota gidan mijinta. Basu da ikon kuma cewa su Yoohan bazasuyi nasu shagalinba tunda shi aure rahama ne, yin shagali a cikinsa kuma ba aibu bane. Abinda kawai ba’a bukata wuce gona da iri da yin almabazaranci da dukiya. (Wadda a yanzu hakan ne yafi yawa a bukukuwanmu. shiyyasa tun a filin bidi’oin ake zazzage daraja da albarkar auren atafi da gayyar sheɗanu😪🤦🏻).
Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “Tom shikenan. Amma bara na fara kiran Yaya (baba malam) na sanar masa tukunna”. Wannan ɗabi’ar tasu na birge Yoohan matuƙa.
Bayan Abbah daya koma gefe ya gama waya da Baba malam ya dawo yana faɗin, “Shikenan zasu zauna ɗin, amma yanzu su fito muje idan lokacin yayi sai a kaisu can. Idan mun koma sai ƴan uwanta suzo su tayata zama su yanzun”.
“Muna godiya Uncle, ALLAH ya ƙara girma”.
Murmushi kawai Abbah yayi, hakama Papa fuskarsa kamar gonar auduga.

★★★★★★

Tun bayan magriba mai kwalliya tazo yima Aymah. Amma saita tubure akan sai tayi sallar isha’i. Dole aka haƙura akan hakan, duk da su ƴan bikima harsun fara wucewa inda za’a gudanar da shagalin. Duk yanda taso su Amal su sanar mata wanene mijin sunƙi. Dan Amal da Yusrah da wasu ƙawayen Amal ɗin biyu maƙwaftansu suna nan tare da ita. Adawiya kam batazo ba wai kanta ke ciwo tasha magani sai anjima zata biyo su Aunty hibbah. Hakan bai wani damu Aymah ba, dan ita mantawa take ma da babin wata Adawiya yanzun.
Bayan an idar da sallar isha’i aka rangaɗama amarya Nu’aymah kwalliyar garari. Dan ko makaho ya taɓa saiya jinjina. Hakama su Amal an musu tasu. Momy daketa danne zuciyarta bisa shawarar ƙawartace da kanta ta kawoma Aymah rigar da zata saka wadda garariya garara har ƙasan amuruka akaje sayota daga aljihun papa da umarninsa.
Nu’aymah taso yin gaddamar sakawa. Amma yanda Momyn ke mata da lallashi ita da ƙawarta ya sakata amsa ta saka ganin rigar akwai hannu a jiki. Ammafa ta bala’i-bala’in haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. Farace tas sai kwalliyar furanni pitch color data ƙawata rigar. Hakan yasa dogon takalminta da shi kansa abin kallone ya kasance pitch. Sarƙa ɗankwali duk pitch. Humm lamarinfa ba’a cewa komai. Ita da kanta Aymah tasan ta haɗu, sai dai zuciyarta a raunane take, dan ta tabbatar ba Yah Ab ɗinta bane angonta. Musamman data san danginta basa irin wannan shirmen bidi’ar, kuma tasan ba Yah Naser bane shima, dan da ace shine katsina za’a kaita. ‘Ni Zainab wanene iyayena suka bama ni’ ta faɗa cikin zuciyarta tana kukan zuci, a fili kuwa idanunta sun cika da ƙwalla. Tayi jarumta sosai wajen ganin basu zubo ba.

Tare suka tafi dasu madam Chioma a mota ɗaya, dan shi ango yana acan hotel ɗin da za’ayi dinner ɗin, acan suke zaune da abokansa da baƙi da shi kansa wasu ma baisan da zuwan nasuba sai da sukazo ɗin. Dan ba ƙaramar gayya su Rich suka yo ba. Harda abokansu tunna secondary skull.
Lallai biki yayi biki kam, dan tun a ganin zuƙa-zuƙan motocin dake cike da harabar hotel ɗin har waje zaka san eh lallai manya ne ke lokacinsu. Ga ƴan jarida da ƴan sanda a wajen harda soji.
Momy da ƙawarta ne kawai suka fita. Aymah kam zata jira angonta. Su Yusrah ma dake motar bayansu duk sun fito suna tsaye. Ba’a rufa mintuna biyarba sai ga Doctor Yoohan mai zamani ya fito tare da gayyar abokansa. Tab, lallai kam ita ranar aure ta musamman ce ga kowa. Duk da shigar suit ɗabi’arsa ce sai yau tafi ta kullum. A kallo ɗaya zaka gane cewa kuɗaɗe masu nauyi aka zuba wajen sayen kayan. Fararene tas shima sai shirt ɗin ciki ce kaɗai ta kasance pitch. Gashin kan nan nasa da saje sunsha gyara sai walƙiya da ɗaukar idanu sukeyi. Duk da fuskar babu murmushi a sake take bai ɗaure ta ba. Hakan ya saka ƙyawunsa sake fita da ƙyau, ga wani irin kwarjini na angwanci dana ruwan alwala daya fara bin ƙofofin gashinsa na ɗawainiya da shi. Duk da ƙyawun da abokansa sukayi suma duk sai ya damasu ya shanye saboda darajar hasken musilinci.
Solomon yay saurin buɗe masa motar da Aymah ke a ciki zaune tanata haɗiyar zuciya. Baice komai ba sai matsawa da yayi jikin motar. Ya ɗan ranƙwafa kaɗan yanda zai iya ganinta da ƙyau. A tare hancinansu suka shaƙar musu ƙamshin turaren juna. Kowanne zuciyarsa ta harba kaɗan, musamman ma Yoohan da ƙyawun da Aymah tayi ya nema zarar da shi a tsaye. Amma a fili sai ya fuske abinsa ya miƙa mata tattausan tafin hannunsa, cikin harshensa da baya fita da ƙyau yace, “Bismillah”.
Wani irin harbawa da ƙarfi ƙirjin Nu’aymah yayi a karo na biyu, duk da kuwa dama ta tsargu tun jin ƙamshin turarensa. Amma sai bata kawoma ranta shiɗinne ba….. Kafin ta fahimci ruɗanin da take neman afkawa taji ya saƙala hannun nasa cikin nata.
Da sauri taja zata fisge jikinta na wani irin tsuma. Riƙesa yayi da ƙyau tare da matso fuskarsa gab da tata. A cikin kunnenta yace, “Wlhy kina min tsiwankin nan sai wannan ya shiga jikinki, garama ki nutsu mubar wajen nan lafiya”. Yay maganar yana nuna mata syringe da batasan daga ina ya cirosa ba.
‘Innalillahi….’ Aymah kawai ke iya maimaitawa a cikin zuciyarta. Kanta ya sake shigewa a ruɗani har batasan lokacin daya fiddota waje ba, ta dai ganta akan ƙafafuntane kawai dake sanye da dogon takalmi. Sauƙinta ma ta iya tafiya dasu dama can, amma da ansha kunya yau.
Gaba ɗaya ta zame masa mutum-mutumi, binsa kawai take duk yanda ya juyata. Ƴan jarida da abokansa da duk suka rikice sai zuba musu hotuna suke tako ina. Hasken camaras kawai kake gani babu ƙaƙƙautawa.
Duk da a cikin abokansa wasu na ganin Nu’aymah tayi kanƙanta hakan bai hanasu taya abokin nasu murna ba da mamakin inda ya samo wannan ƴar shilar. Yoohan dai ya fuske abinsa, dan bayason yayi wani ɗan sakaci da Aymah zata birkice masa a wajen nan. A haka suka shiga cikin hall ɗin daya haɗu harya gaji, decoration ɗin wajen ma komai fari ne da kwalliyar pitch kaɗan-kaɗan. Gashi komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, ga uban haske tako ina tamkar rana. Ko allura ka yadda zaka ɗauka abarka. Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. Ita dai kanta na a ƙasa ne bata yarda ta kalli kowa ba duk da uban tafi da ake musu, ga wata waƙar na tashi a hankali cikin hall ɗin. Bayan an musu rakkiya inda ya dace su zauna kowa ya nema wajen zama. Papa ya gudanar da addu’a a wajen da kansa, shidai Yoohan yayi tasa a cikin rai. Nu’aymah ma sunayi tanayin tata cike da takaici. Ita abinda yafi birkitata shine su baba malam basu san Yoohan arne bane suka aura mata kenan? (Kusanfa ita batasan Yoohan ya musulinta ba) wannan bahagon tunanin ne yake neman zauta mata ƙwalwar kai. Shiyyasa tai shiru bata sake koda wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba har aka fara gudanar da abinda ya tara mutane. Ita dai komai a shirme ma take kallonsa, sai dai ta ɗanji sanyi a ranta lokacin data ɗaga kai idonta ya sauka akan ahalinta su aunty hibbah da sukazo wajen daga baya. Amma saboda girmamawa a garesu sai aka kawosu gaba inda aka tanadar musu tebiri biyu dama. A yanzunma bataga Adawiya ba tare da su.
Lokacin da akace su yanka cake tasha uban takaici. Dan ƙin basa tayi. Idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta ganin yanda hall ɗin yay tsit kowa ya zuba musu idanu. “Kinason muji kunya wajen waɗan nan ɗunbin mutanen da suka taru saboda mu ko? To idanfa kinƙi yin yanda akace ALLAH saina miki abinda sai kin kasa fita hall ɗinnan da kafafunkin nan”.
Gabantane ya faɗi. dan tasan zai iya aikatawar. Tunda har baiji nauyi ko shakkar mata kiss a gidansu ba. Sai da taɗan hararesa ta gefen ido sannan ta ciri cake ɗin da suka yanka ɗin, batare da ta yarda ta kallesa ba takai hannunta bakinsa. Hannun ya kama da nasa hannun ya ƙarasa da cake ɗin cikin bakinsa. Ɗan kaɗan ma ya gutsira ya juya hannun nata dake riƙe a cikin nasa wajen nata bakin. Badan ta so ba ta buɗe kaɗan itama danta ɗan gutsirar sai ya tura mata shi gaba ɗaya tsabar neman rigima. Saurin ɗagowa tai a ɗan zabure, hakan yasata gullewa tai gefe zata faɗi yay azamar riƙo ƙugunta ta dawo kan ƙirjinsa. Tuni tsiwar mutuniyar taku ta motsa, ta ɗago birkitattun idanun nan nata da suka sake girma ruwan hawayen da suka taru a ciki suka sasu wani kala ta musamman. Cikin nasa manyan idanun suka shige caraf, ya sarƙeta da su yanda ya hanata koda motsi suka cigaba da tsaiwa a haka tana a jikinsa idanunsu sarƙe cikin na juna. Gaba ɗaya tama rasa wane kalar bore zatai masa yasan halin da take ciki akan ganinsa matsayin wai miji a gareta. A hankali ta motsa laɓɓanta zatai magana. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓansa. a hankali yace, “Shiiii!!!”. Kasa yin maganar kuwa tayi batare da tasan dalilin hakan ba. Sai ma wata iriyar kasala data saukar mata da bala’in kwarjininsa da bata taɓa ganiba cikin idanunsa.
Kusan a tare hall ɗin ya ɗauki dariya, sai uban hasken camaras kake gani nata walwala su. Dan yanda suke a tsayen dolene su birge mai kallo, musamman ma’abota son soyayya.
Saurin yin ƙasa da kai Madam Chioma tayi tare da saka handkerchief ta share hawayen da suka cika mata idanu, badan shirin da suka ƙulla akan yarinyar nan ba ita da ƙawarta da tun a wajen nan saita halakata ta huta akan yaronta da takejin tsananin kishi. Miracle ma tsaki tayi ta miƙe ta fice daga cikin hall ɗin tana kuka, daga nan sai gidan barasa, dan tana buƙatar sheƙe wasu kwalabe ko zata sami nutsuwa. Hakama sauran ƴammatansa da baisan da zamansu ba abun yamusu takaici, ko joy da take ƙanwarsa sai da ranta ya sosu duk da kuwa sun birgeta itama.
Da sauri Nu’aymah data dawo hayyacinta saboda maganar mc tai saurin saka hannayenta ta ɗan turasa. Sakinta yay badan yaji turawar datai masa ba, sai dan kawai muguntar da tazo masa a cikin rai. Baya ta sakeyi zata faɗi ya riƙo hannunta da sauri ta kuma dawowa jikin nasa. Ya ɗan tsuke fuska kaɗan yana faɗin, “Silly girl”. Sannan ya saketa a hankali. Baki ta murguɗa masa kaɗan tana gyara tsaiwarta zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri. Kallo ɗaya taima sashen dasu Ananah suke ta maida idonta ƙasa ta duƙar saboda tsananin jin kunyarsu data lulluɓe ta.

Haka dai taro ya tashi lafiya bayan anci an sha kamar ba’asan ciwon kuɗi ba. liƙi kam sai kace basu sa zafin nema ba. Dan ƴan dubu-dubu ne sabbi ƙal keta farfar a ƙasa. Musamman lokacin da ango da amarya suka fito filin rawa. Sai dai sunyi tsayene babu wanda ya motsa, dama can kowa yasan Yoohan baya rawa, to bare Aymah da basa samun wannan sakewar a nasu gidan dama.
Su Osin abokan ango dai dasu Gebrail ƙannen ango an cashe gwargwadon iko. Mawaƙan da sukayi wasa a wajen sun kwashi kuɗi kam gwargwadon iko. Ƙarfe ɗaya dai-dai aka tashi.
Wasu sun nufi gidajensu ne, wasu kuma anan hotel ɗin, sai masu komawa gidansu Yoohan da amarya. Su Amal dai binsu Aunty Ananah sukayi suka koma gidan Abbah kamar yanda Omar ya tasasu a gaba…………✍

 

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply