Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 8


Saran Boye 8
Viral

No. 8

……………….Doctor na isowa aka maida Nu’aymah bedroom ɗin Hajjo. duk fita sukai suka bashi waje yay aikinsa yanda ya kamata. Sai Abubakar da aka bari kawai dan ya taimaka masa da wani abun idan ya buƙata.
Sunyi jigum-jigum a falon Hajjo, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa wadda ALLAH kaɗai yasan minene a cikinta.

Juyawa baba malam yay a hankali ya fice daga sashen. Sashensu ya nufa dan sai yanzune hankalinsa ya kai ga rashin ganin Umm tare da su. Babu kowa a falon, ya nufi bedroom ɗinta canma babu kowa. Fitowa yay ya nufi nasa ɗakin ko tana can. Sai dai kuma nanma babu kowa. A ɗan ruɗe ya dawo ɗakin Muh’d. Muhammad ɗin kawai ya samu yana canja Uniform ɗin islamiyya dan yanzun suka taso. Baima gansaba, sai da yace, “Muhammad ina Umm ɗinku?”
Jiyowa Muhammad yay da sauri, fuskarsa da ɗan damuwa yace, “Abba nima ban gantaba, na shiga ko ina bata nan kuma yunwa nakeji”.
Shigowa sosai Baba malam yay cikin ɗakin idonsa akan Muhammad ɗin. “Yunwa kuma Muhammad? Bakaci abinciba ka fita ne?”.
“Abba lokacin nasha fura wajen Hajjo na ƙoshi, yanzu kuma zanci”.
Kama Hannunsa Baba malam yay suka fita kitchen da tsammanin zaiga Umm a can. Sai dai kuma mai aikinta kawai suka samu tana gyaran kayan miya. Cike da girmamawa ta gaida Baba Malam ɗin. Amsawa yay yana cirar tuffah dake cikin fruit tray ɗin da suke sakawa. Ƙarasawa yay wajen fanfo zai wanke Saude tai saurin faɗin, “Baba malam kawo a wanke”. Baiyi musu ba ya miƙa mata tuffa ɗin guda biyu daya ɗauka. Sake bin kitchen ɗin yay da kallo kafin yace, “Ina Jannat ɗin take na ganki ke kaɗai kina aiki?”.
Saude data wanko apple ta ɗaura a ƙaramin filet tace, “Nima na shigo ban gantaba, dama naje can ƙasan layine na sayo mata daddawa data bada. To nadawo kuma na duba kamar ta fita, shine nace bara na gyara ko kayan miya kafin ta dawo”. Shiru Baba malam yayi gabansa na faɗuwa. Amma sai ya danne ya kalli Muhammad dake saurarensu. Filet ɗin tuffa ɗin ya miƙa masa yana faɗin, “Karɓa wannan kaje kaci muje salla mu dawo saika zauna cin abincin”.
Kai Muhammad ya ɗaga masa da amsar filet ɗin. Yaron nagaba yana biye da shi har suka fice. Sake komawa yay ɗakin Umm ɗin dai zuciyarsa na bala’in harbawa. Tsaye ya isketa gaban Wadrobe tana fiddo kaya da alama wanka tayo. Ya sauke ajiyar zuciya da faɗin ‘Alhmdllh’ a fili. Hakanne yasata juyowa da sauri dan bataji shigowarsa ba. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru tana kallonsa kawai.
“Naje massallaci”. ya faɗa a taƙaice yana juyawa ya fita daga ɗakin. Binsa da kallo Umm tayi harya ɓace mata sannan ta ɗauke kanta hawaye na ziraro mata.

★★★★

A ɓangaren Hajjo Doctor ya bama Nu’aymah dukkan taimakon daya dace kamar yanda ya saba a duk lokacin da ciwon nata ya motsa. Sai dai yau ta jima bata farfaɗo ba. Dan sai da sukaje sukai sallar magriba suka dawo sannan ya ƙarasa ƴan dabarunsa cikin amincin ALLAH ta farfaɗo.
Godiya yayma UBANGIJI tare da fita ya sanar musu ta farfaɗo. Dan yau ana idar da salla gaba ɗayansu suka baro massallaci, baba malam ne kawai yay zamansa. Matanma suna idar da sallar duk nan suka sake dawowa harda yaransu da dawowarsu islamiyya sukaji komai.

Bayan Doctor ya kammala komai ya buƙaci tattaunawa da su Abbah. Da ƙyar suka samu Baba malam ya baro massallaci yazo.
Doctor ya gyara zamansa cikin girmamawa a garesu yace, “Gaskiya wannan karon jikin Nu’aymah yayi tsamari. Kunsan matsalarta ba’aso abu yana firgitata da tsanani. tsawa da duhu suna gaba-gaba wajen girmama ciwonta da ƙarfafa shi”.
Hajjo ce tai saurin faɗin,  “Hakane likita, duk munsan wannan, kuma ana ƙoƙarin kiyayewa. Yau ɗinma kuskure aka samu kasan ajizanci na ɗan adam. Yanzu minene mafita?”.
“To Hajjo ALLAH ya kiyaye gaba, amma kam yau abin yaso yin tsamari sosai a gareta, dan yanzu haka zancen da nake muku sam bata cikin hayyacinta, fatanmu dai ta dawo hayyacinta lafiya batare data manta komaiba ma bayan ta farka”.
Da matsanancin tsoro suke kallonsa, sai dai kowa ya kasa magana. Da sauri yace, “Bamu da tabbacin hakan, komai na ALLAH ne, mucigaba da mata addu’a insha ALLAHU zata farko cikin ƙoshin lafiya. Dama inada shawara ne, dan tun kwanaki naso zuwa da zancen sai nai tafiya kuma, yau kwanana shidda kenan da dawowa ma, zan kuma iya komawa a koda yaushe dan na samu gurbin ƙaro karatu a ƙasar Australia ne”.
A tare sukace, Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka ya bada ikon karanto abu mai amfani”.
“Amin ya rabbi, nagode sosai”.
Abbah Musbahu yace, “Muna surarenka. Wane shawarace da kai?”.
“Dama akwai wani likita babba kuma ƙwararre, dan kam ALLAH ya hore masa baiwa ta fannoni da dama inhar a ɓangaren likitancine. To wani abokina ya tabbatar min har masu irin ciwon Nu’aymah yana basu taimako. Matsalar ɗaya ce, shine ganinsa. Ganinsa nada matuƙar wahala dan yana aikine a Nigeria da wajen Nigeria. Ko a yau zai iya shigowa kano ya duba marasa lafiya ya fice, zuwa dare kuma kaji bama ya ƙasar gaba ɗaya”.
“To ai mu Doctor ko biyansa ya kama muyi sai muyi dan yazo ya duba ta”. Cewar Abban Abdallah.
“Ai anan gizo ke saƙar Malam. Dan ko nawa za’a biyashi bazaizo gida duba mara lafiya ba. Dolene sai dai mutum yaje yay tanadin ganinsa kamar kowa, zai baka date ɗin da zaka gansa idan har ciwonka yakai shi zai dubaka, idan kuma yaga akwai mafita zai haɗaka da wani likitan da zakaje ka gani. Date ɗin da za’a rubuta maka kuma dole a sannan ne zaka gansa babu alfarma. Kwanaki yaron president ya samu wata babbar matsalar da sai shine ake fatan ya dubasa ko za’a dace. Har jirgi aka aika ya ɗakkosa daga wata ƙasar dan kawai yazo ya dubashi amma yace suje su sai kati subi layi kamar yanda kowa keyi shi bazaije ba. Kuma dole hakan akayi”.
Babu wanda bai jinjina wannan al’amari ba a cikinsu, sukai shiru kowa na tunanin mafita kuma. Ganin haka Ahmad yace, “To Doctor idan babu damuwa ai muma sai kai mana hanya mubi hanyar data dace ɗin na ganin nasa kawai, ko’a ina yake mu zamu bisa insha ALLAH. Fatanmu dai a dace”.
“Hakan shine dai-dai. Ga Number ɗaya daga ma’aikatansa zan baku sai ku nemesa, insha ALLAH zai muku ƙarin bayanima fiye da nawa ma, ga kuma ta abokina ma duk zan haɗa muku shima likitane zaku iya neman taimakonsa koda ni na wuce ne”.
Rubutawa yay ya miƙama Hajjo dake a kusa da shi, ita kuma saita miƙama Baba malan da tun shigowarsa baiyi ko tari ba. Bai musaba ya amsa ya ajiye gefensa da nufin idan ya tashi sai ya ɗauka yaje ya adana. Doctor ya tattare file ɗin bayanan ciwon Nu’aymah waje guda ya sake mi[6/13, 10:48 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply